Marwa ya gargadi jami’an NDLEA game da tsare mutane ba bisa ka’ida ba, kama masu garkuwa da mutane
Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa (Mai murabus) ya bayyana godiyar hafsoshi da jami’an hukumar yaki da muggan kwayoyi ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da ba da goyon baya ga ci gaban da ake samu na kokarin dakile matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar su a kasar.
Marwa ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a lokacin da yake duba kayayyakin aiki a barikin hukumar da ake ci gaba da ginawa, wanda ake sa ran za a fara aiki da shi nan ba da jimawa ba a Yola jihar Adamawa.
Hakan ya fito ne daga bakin Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hedikwatar hukumar a Abuja, Femi Babafemi, a ranar Juma’a.
Marwa ya gode wa Allah da samun nasarar wannan aikin, ya kuma yaba da yadda gwanatin yanzu ke ci gaba da gudanar da mulkin daga inda gwamnatin baya ta tsaya.
Ya ce, Shugaba Buhari ya yaba da al’amuran da suka shafi tsaro da jin dadin ma’aikata da suke kamawa, gurfanar wa da kuma magance masu laifi, duk da cewa masu laifin daga baya suna komowa su zauna a cikin su. “Amma yanzu muna da bariki na jami’an mu.”
Marwa ya bayyana cewa, Shugaba Buhari ya amince da yin barikin, kuma shi ya fara shi, A yanzu kuma Shugaba Tinubu ya ci gaba da irin wannan kishi da himma, don haka mun yaba da wannan al’amari na nuna damuwa ga Hukumar NDLEA.”
Marwa, ya yaba da irin aiki da ingancin aikin da ake yi a barikin.
“Masu ba da shawara, ’yan kwangila sun yi aiki mai kyau, mai inganci, sun sa ido sosai, sun yi aiki da mafi kyawun kayan aiki kamar yadda kuke gani, kuma mun yi kashi casa’in da biyar cikin dari na wannan. Muna fatan da yardar Allah kafin tsakiyar wannan shekarar za mu kaddamar da wannan kason na farko.”
“Da farko muna da shiyyoyi shida a ƙasar nan, muna da burin samar da bariki a kowannen su, domin samun daidaito kowacce shiyyar ta samu, kuma a cikin shekaru masu zuwa, muna fatan gwamnatin da za ta gaji wannan za ta ci gaba da bin dukkan dokokin jihohi talatin da shida har da babban birnin tarayya da kuma reshen na musamman na wannan hukumar.”
“Jami’an mu duk sun ji dadi, kuma suna da zimmar kara kwazo domin samun nasara bisa aikin su, domin wannan ya nuna irin kyakkyawan aikin da jami’an suke ne wanda ya samar da wannan aiki kuma a shirye suke su kara yin hakan,” inji shi.