Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO) ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da jarrabawar kammala sakandare (SSCE) a ƙasar Saudiyya.
Hakan ya biyo bayan amincewar da wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Ƙaramin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu da Magatakardar NECO, Farfesa Ɗantani Wushishi, suka yi wa makarantar Nigeria International School, Jeddah.
Wata sanarwa ɗauke da sa hannun Muƙaddashin Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Zamani na NECO, Azeez Sani a ranar Asabar, ta ce a yayin ziyarar, tawagar ta gudanar da tantance kayan aikin makarantar.
Sununu a jawabinsa, ya umarci ma’aikata da ɗaliban makarantar da su ci gaba da zama jakadun Nijeriya nagari ba a ƙasar Saudiyya kaɗai ba har ma da ɗaukacin Ƙungiyar Haɗin kan Ƙasashen Yankin Larabawa.
Ya ce bayan da aka yi nazari a tsanake kan wuraren koyo na makarantar kamar ɗakin jarrabawa, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu, darussa da tsarin koyo da tsaro baki ɗaya, an gano makarantar ta cancanci a yi la’akari da ita a matsayin cibiyar NECO SSCE ta cikin gida.
Ya ce bayan tantancewar da aka yi, a sakamakon haka an ba wa makarantar cikakken amincewa.
A nasa ɓangaren, Magatakardar Hukumar ta NECO, Farfesa Wushishi, wanda ya ba da taƙaitaccen tarihin ci gaban NECO, ya bayyana wa mahukunta da ma’aikatan makarantar muhimmancin amincewar makarantar.
Wushishi ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da cewa makarantu sun samu isassun wuraren koyarwa da koyo da suka dace da jarabawa.
Tun da farko dai tawagar ta samu tarba ne a lokacin da ta isa makarantar daga Babban Jakada, Amb. Bello Kazaure da Shugaban Makarantar, Alhaji Abdulkadir Maikuɗi da sauran ma’aikatan.
Ministan da magatakardan NECO sun kuma ziyarci gidan Nijeriya da ke Jeddah, inda suka tattauna da Babban Jakada da sauran ma’aikatan ofishin jakadancin.
NECO tana da sauran cibiyoyin jarrabawar ƙasa da ƙasa a ƙasashen Togo, Jamhuriyar Benin, Equitorial Guinea, Nijar da Jamhuriyar Gabon.