Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya, (NEDC), ta sanar da gaggauta sakin buhunan shinkafa da sauran kayayyakin abinci 300,000 ga mazauna yankin arewa maso gabas.
Manajan daraktan hukumar, Mohammed Alkali, a wata ganawa da manema labarai jiya a Abuja, ya ce sakin wani ɓangare ne na ɗaukar matakan tallafawa ƙoƙarin gwamnatin tarayya da na jihohi a yankin don rage matsalar tattalin arziƙin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
Shugaban hukumar, Manjo Janar Paul Tarfa (mai ritaya) ya ce hukumar ta gano hanyoyin da za a bi domin rage wa ‘yan ƙasar raɗaɗin halin da suke ciki a yankin Arewa maso Gabas.
“Muna so mu ci gaba da ayyukan da za su inganta ayyukan zamantakewa da tattalin arziƙi a faɗin yankin da buɗe kasuwanni da hanyoyi don haɗa yankin,” inji shi.