Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa ma’ajiyar kayayyaki da aka wawashe a Abuja ranar Lahadi ba nata ba ne.
Mazaunan da ke fama da yunwa sun shiga wani wurin ajiyar kaya da ke unguwar Gwagwa a Abuja ranar Lahadi, inda suka yi awon gaba da kayayyakin abinci da aka ajiye.
Mazauna yankin sun ce da sanyin safiyar Lahadi ne wasu matasa suka kutsa cikin ma’ajiyar da ke anguwar Tasha, inda suka yi awon gaba da buhunan masara da sauran hatsi.
Wasu sun ce mazauna ƙauyukan Jiwa da Karmo da ke maƙwabtaka da su sun yi dafifi zuwa wurin da nufin cin moriyar abin.
“Wannan domin a fayyace cewa ma’ajiyar da aka wawashe ba na NEMA ba ne.
“Duk da haka, hukumar ta jajantawa masu ma’ajiyar da aka yi satan,” Kakakin Hukumar NEMA, Mista Manzo Ezekiel, ya bayyana haka a ranar Lahadi a Abuja.
“Babban darakta, Mista Mustapha Ahmed, ya umurci Daraktocin Shiyya da Shugabannin Ayyuka, da su ƙarfafa tsaro a ofisoshin hukumar NEMA da ma’ajiyar kayayyaki a faɗin ƙasar nan.
Ezekiel ya ƙara da cewa, “Umurnin shine a daƙile duk wani rashin tsaro a cibiyoyin NEMA a faɗin ƙasar.”