Da yake har yanzu ba a maye gurbin kocin Super Eagles na Nijeriya ba, rahotanni sun nuna cewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta fara duba yiwuwar ɗaukar Herve Renard, kocin da ya jagoranci wani wasan ƙarshe a gasar cin kofin duniya a wannan matsayi.
Herve Renard kuma shi ne koci ɗaya tilo da ya jagoranci ƙasashe biyu da suka lashe gasar cin kofin Afrika (AFCON) bayan da ya jagoranci Zambia ta lashe gasar a shekarar 2012 sannan kuma ya taimakawa Ivory Coast ta lashe gasar a shekarar 2015.
Rahotanni da dama sun bayyana cewa NFF za ta fafata da ƙasashe irin su Koriya ta Kudu da Morocco da Kamaru da sauran su wajen ɗaukan kocin wa Super Eagles ta Nijeriya.
Renard ya jagoranci Faransa zuwa wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta mata na 2023 da Saudiyya zuwa nasarar farko da suka samu a kan Argentina a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar.
Ana sa ran kocin ƙwallon ƙafar Faransa, Hervé Renard, wanda ya jagoranci Saudiyya a gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022, zai yi murabus daga matsayinsa na kocin tawagar ‘yan wasan Faransa a ƙarshen gasar Olympics ta Tokyo.
Renard da kansa ya sanar da matakin da ya ɗauka yayin wani taron manema labarai a farkon wannan makon, inda ya tabbatar da cewa ya riga ya sanar da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa (FFF) game da aniyarsa ta ƙarawa gaba bayan gasar bazara.
Yayin da yake amincewa da wahalar aikin, Renard ya bayyana manufofinsa na gaba, yana mai cewa yana fatan jagorantar tawagar ‘yan wasan ƙasa ta maza zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026. Wannan zai zama gasar cin kofin duniya karo na uku a matsayinsa na kocin tawagar maza, kuma ya jaddada cewa wannan shi ne babban ƙwarin gwiwa a gare shi. Renard yana neman damammaki don ya karɓi ragamar horar da wata tawagar ƙasa ta maza ba da jimawa ba.
A halin da ake ciki, tsohon kyaftin ɗin Super Eagles kuma kocin tawagar, Sunday Oliseh, ya musanta batun neman muƙamin koci a Super Eagles, kuma ya soki tsarin neman aikin.
Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bayyana babu kowa a matsayin kocin Super Eagles makonni biyu da suka gabata, biyo bayan ƙarewar kwantiragin tsohon kocin, Jose Peseiro bayan kammala gasar AFCON a ƙasar Ivory Coast.
A wata talla da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, NFF ta yi kira da a nemi aikin tare da wa’adin ranar 13 ga Maris.
Hukumar NFF ta bayyana cewa mai horar da ‘yan wasan Eagles “dole ya tabbatar da ƙwarewa a matakin wasan ƙwallon kafa.” Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta NFF ta fitar da sunayen masu horarwa sama da 50 waɗanda za su yi aikin.
“Ban nemi aikin Eagles ba, rahotannin da suka bayyana haka ƙarya ne,” inji Oliseh a wata hira da jaridar Punch.
“Na bayyana cewa idan Nijeriya na buƙatar taimako na a matsayina na koci zan kasance a shirye in taimaka idan yanayin ya yi daidai. A shirye nake don taimakawa Nijeriya amma ban nemi aikin ba.”
Oliseh, wanda ya gaji marigayi Stephen Keshi a matsayin kocin Eagles a shekarar 2015, ya soki tsarin neman aikin na Eagles.
“Bari mu kalli abun haka, lokacin da Jurgen Klopp ya fito a watan da ya gabata ya sanar da cewa zai bar muƙaminsa na kocin Liverpool, shin kun ji ko karanta a ko’ina cewa kulob ɗin ya ba da sanarwar cewa masu horarwa su nemi aikin? Abu ɗaya da su (Liverpool) suke yi a halin yanzu shi ne suna neman kocin da ya dace da falsafa da salon su.
“Idan mu (Nijeriya) ba za mu iya baiwa masu horarwa ‘yan asalinmu damar taimaka wa ƙwallon ƙafar kasar ba, to wa zai iya?”
“Kowa ya san ni mai bayar da shawarar koci ‘ɗan asalin ƙasar ne don ya jagoranci Eagles, waɗannan biyun (Amuneke da Finidi) suna da kyau ga aikin. Duk wanda ya fahimci ƙwallon ƙafa da gaske zai san cewa Eagles ba sa buƙatar koci na ƙasashen waje.
“Ina adawa da kocin ƙasar waje wa tawagar ƙasarmu. Koci na cikin gida ne ya lashe AFCON wa Ivory Coast da wanda ya ci wa Senegal a baya.”