Back

Nijeriya ta buɗe iyakokin ƙasa da na sama da jamhuriyar Nijar, ta kuma ɗage wasu takunkumi

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarnin buɗe iyakokin Nijeriya ta kasa da ta sama da jamhuriyar Nijar tare da ɗage wasu takunkumin da aka ƙaƙabawa ƙasar.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, umarnin ya yi daidai da shawarar da hukumar ta Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka ta yanke a babban taronta na musamman da ta gudanar a ranar 24 ga watan Fabrairun 2024 a Abuja.

Shugabannin Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka sun amince da ɗage takunkumin karya tattalin arziƙi da suka ƙaƙabawa Jamhuriyar Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea.

“Shugaban Ƙasar ya ba da umarnin a ɗage takunkumin da aka sanya wa Jamhuriyar Nijar nan take:

(1) Rufe iyakokin ƙasa da na sama tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka a duk jiragen kasuwanci da ke zuwa ko kuma daga Jamhuriyar Nijar.

(2) Dakatar da duk wani hada-hadar kasuwanci da hada-hadar kuɗi tsakanin Nijeriya da Nijar, da kuma dakatar da duk wasu hada-hadar hidima da suka haɗa da ayyukan amfani da wutar lantarki zuwa Jamhuriyar Nijar.

(3) Daskarar da kadarorin Jamhuriyar Nijar a Babban Bankin Kungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka da kuma daskarar da kadarorin Jamhuriyar Nijar, da kamfanonin gwamnati, da ma’aikatu a bankunan kasuwanci.

4) Dakatar da Nijar daga duk wani tallafi na kuɗi da mu’amala da duk hukumomin kuɗi musamman EBID da BOAD.

(5) Hana tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da ‘yan uwansu.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Shugaba Tinubu ya kuma amince da ɗage takunkumin kuɗi da tattalin arziƙi da aka ƙaƙabawa Jamhuriyar Guinea.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?