Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya tabbatar da cewa Nijeriya ba za ta ƙara buƙatar shigo da man fetur daga watan Yuni, 2024 ba.
Matatar mansa da ke Nijeriya, za ta biya buƙatun man fetur da dizal na Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka, tare da biyan buƙatar man jirage na nahiyar.
Dangote ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na shugabannin kamfanonin Afirka da aka yi a Kigali, inda ya bayyana ƙwarin guiwar sauyin da ke tafe a fannin makamashin Afirka.
Ya bayyana cewa matatar ta na da ƙarfin samar da man fetur da dizal na Yammacin Afirka, da kuma buƙatar man jirage na nahiyar, tare da fitar da rarar man fetur zuwa ƙasashen Brazil da Mexico.
Ɗan kasuwan ya kuma bayyana ci gaban da kamfanin man ya samu na tabbatar da cewa Afirka ta zama mai dogaro da kanta a fannin makamashi.
Ya ƙara da cewa matatar ta na da burin sarrafa ɗanyen mai na Afirka da kuma samar da man da aka tace ba kawai a cikin Nijeriya ba har ma a faɗin Afirka baki ɗaya.
Duk da ƙalubalen da ake fuskanta wajen gina matatar, musamman daga waɗanda suka saba da halin da ake ciki, Dangote yana da ƙwarin gwuiwa game da yuwuwar Nijeriya ta zama mai taka muhimmiyar rawa a fannin makamashi a Afirka.
Ya yi kira ga shugabanni da su sake nazari da goyon baya don tabbatar da samun sauƙin kasuwanci a nahiyar.