Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) da gwamnatin jihar Jigawa sun horar da mutane 1,000 a fannonin fasahar zamani.
Darakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa, da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ya yi kira ga matasa a jihar da su rungumi basirar fasahar sadarwa (ICT) saboda muhimmancinta don ci gaban tattalin arziƙin ƙasa.
Yayin da yake ba matasa shawara a ƙasar nan da su rungumi fasahar ICT domin samun ci gaba mai ɗorewa da kuma dogaro da kai, shugaban NITDA ya bayyana cewa duniya na sauya sheƙa daga cancantar takarda zuwa fasahar zamani kuma waɗanda suke son yin nasara dole ne su ba da himma domin su rayu.
Ya ce, “Wannan horon da aka bai wa matasa dubu ɗaya da ke Jigawa kan ƙwarewa a fasahohin zamani zai bai wa jihar damar dawo da martabar da ta ɓata a matsayin jihar dake gaba a fannin ICT a Nijeriya a farkon shekarun 2000.”
A cewar Darakta Janar ɗin, NITDA za ta ci gaba da yin haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi a faɗin ƙasar nan don faɗaɗa ilimin fasahar zamani na ƴan kasa wajen ci gaban tattalin arziƙin fasahar zamanin ta ƙasa don yaƙi da talauci da ƙalubalen da ke da alaƙa da talauci a ƙasar.”
Yayin da yake jaddada muhimmancin horaswar wanda Hukumar Tallafawa Matasa ta gwamnatin jihar, NITDA, Jami’ar Base, da IDEAS Hub suka shirya, Inuwa ya bayyana ta a matsayin dabarar ƙoƙarin jihar na neman ƙarin damammaki na tattalin arziƙi domin haɓɓaka ci gaban jihar.
Gwamna Umar Namadi, wanda mataimakin gwamnan jihar, Aminu Usman Gumel, ya wakilta a wajen taron ya yabawa NITDA bisa shirye-shiryenta na shiga tsakani a jihar wanda ya shafi ɓangarori da dama.
Ya yi nuni da cewa, sun taimaka wa jihar wajen samun nasarar da ake samu a halin yanzu cikin ƙasa da shekara guda a ofis.
Sauran waɗanda suka gabatar da jawabai a wajen bikin ƙaddamarwan waɗanda suka haɗa da Darakta Janar na Hukumar Tallafawa Matasa da Samar da Aikin yi ta jihar Jigawa, Dakta Habibu Ubale, da wakilai daga ƙungiyoyin haɗin gwiwa duk sun amince cewa samar da fasahar ICT ga matasan jihar zai bunƙasa ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa.
Horon wanda ya mayar da hankali kan fannoni biyar da kulawa ta musamman ga kimiyyar haɗa na’urar robot, fasahar na’ura mai ƙwaƙwalwa wacce ke kwaikwayon ɗabi’un mutane, da gina manhajar na’urar computer, da dai sauransu an yi imanin cewa zai samar da ƙwararrun matasa waɗanda za su jagoranci ci gaban fasahar zamani a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.