Back

Nollywood ta sake yin jimami yayin da Mista Ibu ya rasu

Tsohon jarumi, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, wanda ake matuƙar ƙaunarsa a fina-finai da barkwanci, ya rasu a ranar Asabar, 2 ga Maris, 2024, a wani asibiti a Legas.

An ce ya samu bugun zuciya. Rasuwar tasa ta zo ne sa’o’i ashirin da huɗu bayan rasuwar wani jarumi, Quadri Oyebamiji, wanda aka fi sani da Sisi Quadri, a jihar Osun.

Da yake jinjinawa marigayi Okafor, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Wasan Kwaikwayo ta Najeriya, Emeka Rollas, ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa, “Ranar baƙin ciki ga Ƙungiyar ‘Yan Wasan Kwaikwayo ta Najeriya. Kate Henshaw ta rasa mahaifiyarta a safiyar yau, kuma Mista Ibu ya samu bugun zuciya, a cewar manajansa na shekaru ashirin da huɗu, Don Nwuzor. Ina baƙin cikin sanarwa cewa Mista Ibu ya rasu. Allah ya sa ya huta.”

Ku tuna cewa ya jima yana fama da rashin lafiya wanda ya kai ga yanke masa ƙafa. Hakan ya biyo bayan kira ga masoyan sa da sauran jama’a da su yi masa addu’a tare da ba shi tallafin kuɗi domin biyan kuɗin magani.

Sai dai kuma a lokacin da jarumin yake kwance a gadon asibiti, ‘yan uwansa sun yi ta gwabza faɗa, inda suke zargin juna da neman sace kuɗaɗen da jama’a suka tara.

Lalle ne, shekarun ƙarshe na ɗan wasan kwaikwayon sun kasance da rikici. A lokuta daban-daban, ya yi ikirarin cewa ya tsira daga yunƙurin guba da dama. A cewarsa, an yi yunƙurin kashe shi har sau uku amma ya tsallake rijiya da baya.

Jaruman da suka rasu a bana sun haɗa da Sisi Quadri da Deji Akinremi, wanda aka fi sani da Olofa Ina.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?