
Nadeem Anjarwalla
Ofishin Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa (ONSA), ya tabbatar da tserewar Nadeem Anjarwalla daga hannun hukuma, wanda ake zargi da aikata laifuka a binciken da ake gudanarwa kan ayyukan Binance, wani kamfani na musayar cryptocurrency.
Mista Zakari Mijinyawa, Shugaban Sashen Sadarwa na ONSA, ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja, cewa Anjarwalla ya tsere ne a ranar Juma’a.
Mijinyawa ya ce ONSA ta ɗauki matakin gaggawa tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin tsaro da ma’aikata, sassa, da hukumomi, tare da al’ummar ƙasa da ƙasa domin kamo wanda ake zargin.
Ya ce jami’an tsaro na kuma aiki da Hukumar ‘Yan Sandan Ƙasa da Ƙasa (Interpol) domin samun sammacin kama wanda ake zargin.
A cewarsa, bincike na farko ya nuna cewa Anjarwalla ya tsere daga Nijeriya ne ta hanyar amfani da fasfo ɗin da aka shigo dashi ta ɓarauniyar hanya.
Kakakin ONSA ya ce an kama jami’an da ke da alhakin tsare wanda ake zargin ne yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin guduwar sa.
Mijinyawa ya ce gwamnatin Nijeriya, kamar sauran ƙasashen duniya, tana gudanar da bincike a kan hada-hadar halasta kuɗaɗen haram da kuɗaɗen ta’addanci da ake tafkawa a dandalin musayar kuɗi na Binance.
Anjarwalla, wanda ke riƙe da fasfo ɗin Burtaniya da na Kenya, shi ne manajan yankin Afirka na Binance kuma wata kotu a Nijeriya ta bayar da umarnin tsare shi na tsawon kwanaki 14.
“An sanya shi sake bayyana a gaban kotu a ranar 4 ga Afrilu.
“Muna kira ga al’ummar Nijeriya da sauran ƙasashen duniya da su bayar da duk wani bayanan da suke da su da za su taimaka wa jami’an tsaro su cafke wanda ake zargin.”