Back

NSCDC ta gano haramtattun matatun mai a dajin Rivers

Ɗaya daga cikin tafkunan da ke wurin haƙar man

Rundunar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya, NSCDC, Reshen Rundunar Leƙen Asiri ta Musamman, ta gano wani tankar man fetur da ya kai lita 500,000 a yankin Odagwa dake ƙaramar hukumar Etche a jihar Rivers.

Kakakin Rundunar NSCDC na Jihar Rivers, Sufeto Olufemi Ayodele, wanda ya gabatar da wasu daga cikin waɗanda aka kama a wani samame da aka kai a wurin da ake haɗa man da ke Odagwa Etche a Fatakwal, ya ce jami’ansu sun gano wasu haramtattun matatun mai sama da 10 tare da kimanin lita 500,000 na ɗanyen mai ƙunshe a cikin haramtattun tafkuna kusan 50 da aka gina. Ya ce an gano hakan ne bisa sahihan bayanan sirri.

Ya ce hukumar NSCDC za ta ci gaba da yin aiki tuƙuru wajen yaƙi da satar ɗanyen mai, haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, haramtattun harkokin man fetur da sauran su a faɗin ƙasar nan.

“Kwamandan Hukumar NSCDC, Dakta Ahmed Abubakar Audi, ya sha nanatawa cewa za a yi yaƙi da duk wasu ayyukan zagon ƙasa ga tattalin arziƙin ƙasa domin kuwa waɗanda ake tuhuma za su fuskanci fushin doka ba tare da la’akari da masu ɗaukar nauyinsu ba.

“CG ya ba wa Rundunar Leƙen Asiri ta Musamman umurnin su kasance masu zurfafawa da masu samar da sakamako a cikin ayyukansu.”

“Bisa ga sahihan bayanan sirri, Rundunar Leƙen Asirin ta Musamman ta gano wasu haramtattun matatun mai na cikin gida guda 10 a cikin dajin da ke unguwar Odagwa a ƙaramar hukumar Etche ta jihar Rivers inda aka kama mutane 5 da laifin tace ɗanyen mai ba bisa ƙa’ida ba,” inji shi.

Ya ce an ga kusan tukwane daban-daban guda 10 masu ƙarfin lita 50,000 tare da babbar injin fanfo guda ɗaya, tankunan karɓa, magudanan roba guda 25 da ake amfani da su wajen fitar da ɗanyen mai da kuma dogayen magudana da yawa masu ɗauke da litar ɗanyen man da ba su cancanta ba da kuma man gas da aka tace ba bisa ƙa’ida ba a manyan tankunan da wasu ƙananan tafkuna guda 20 da aka dasa a ƙasa.

Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama waɗanda ya ce an miƙa su ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike kamar su Favor Chukwu, Desmond Umeh, Godwin Amos, Bineace Galion da Goodnews David.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?