Back

NSCDC ta kama wani mutum da ke ƙoƙarin shiga ɗakin kwanan ɗalibai mata a asirce

Jami’an Hukumar Tsaron Farina Kaya ta Nijeriya (NSCDC) dake aiki da Sashen Kula da Muhimman Kadarori na Ƙasa da Ababen More Rayuwa a Kano sun cafke wani matashi mai suna Muhammad Munzali ɗan shekaru 35 da ke Kaura Gidan Damo a ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano a lokacin da ya ke ƙoƙarin shiga ɗakin kwanan ɗalibai mata a asirce.

A cewar Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, jami’an ’yan banga ne suka cafke wanda ake zargin da misalin ƙarfe 10 na dare a lokacin da ya ke kutsa kai cikin ɗakin kwanan ɗalibai na jami’ar Skyline Nigeria da ke Sardauna Crescent, Nasarawa GRA, Kano.

A cewarsa, wanda ake zargin ya ɓadda kama da rigar mata kuma an same shi da laya a jikinsa.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin kutsawa cikin ɗakin kwanan ɗalibai mata na jami’ar mai zaman kanta.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?