Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, ya caccaki Akanta-Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein, kan taron bita a Landan da ta shirya wa kwamishinonin kuɗi na jihohi.
Obi, a ranar Asabar a wani dogon rubutu a shafinsa na X, ya bayyana cewa dole ne ‘yan Nijeriya su yi kakkausar suka tare da yin Allah wadai da matakin da Ofishin Akanta-Janar na Nijeriya ya ɗauka na gudanar da taron bita a Landan.
“Wannan shawarar ba kawai abin da ba za a yarda da shi ba ne amma kuma yana da matuƙar damuwa a matakai da yawa. Bisa la’akari da irin wahalhalun da ƙasar nan ke ciki da kuma halin tausayin da kuɗin ƙasarmu ke ciki da kuma tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya, duk wani aikin gwamnati a ƙasashen waje ya kai ga rashin tausayi daga ɓangaren gwamnati da duk wata hukuma ko ɗaiɗaikun mutanen da abin ya shafa.
“Na farko dai, yana nuna rashin kula da kasafin kuɗi da kuma kashe kuɗaɗen jama’a cikin tsanaki.
“A daidai lokacin da Nijeriya ke fama da ƙalubalen tattalin arziƙi da suka haɗa da hauhawar farashin kayayyaki, rage darajar kuɗin ƙasar, da kuma ƙarin gibin kasafin kuɗi, bai dace kwata-kwata a yi almubazzaranci da kuɗaɗen masu biyan haraji kan manyan tarurrukan ƙarawa juna sani a ƙasashen ƙetare ba,” inji Obi.
Ya ce kamata ya yi a karkatar da kayayyakin aikin da aka ware domin irin waɗannan dalili wajen magance matsalolin da ke addabar cikin gida kamar kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa da kuma kawar da fatara.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kuma ce taron bita a birnin Landan ya aika da saƙon da bai dace ba ga al’ummar Nijeriya da ƙasashen duniya.
“Yana ci gaba da sanya tunanin cewa jami’an gwamnati na yin almubazzaranci da dukiyar talakawa.
“Yana samar da al’adar son kai da nesanta kansu daga abubuwan da talakawan Nijeriya ke fuskanta a kullum, waɗanda ke fafutuka a kullum don samun biyan buƙatun rayuwa a cikin tsadar rayuwa da ƙarancin damar samun muhimman ayyuka.
“Bugu da ƙari, akwai tambayoyi masu muhimmanci game da wajibci da ingancin gudanar da taron bita a ƙasashen waje, musamman a birni mai tsada kamar London,” inji Obi.
Ya yi nuni da cewa Nijeriya na da ƙwararrun ma’aikata da kwararru da dama waɗanda zasu iya bayar da horo da ƙwarewar da ake buƙata.