Shugaba Vladimir Putin ya lashe zaɓen da aka yi a Rasha a ranar Lahadi, inda ya tabbatar da cewa ya riga ya riƙe madafun iko a nasarar da ya ce ya nuna cewa Moscow ta yi daidai da ta tsaya tsayin daka kan ƙasashen Yamma da tura dakarunta cikin Ukraine.
Putin, wanda tsohon Laftanar Kanal ne na KGB, wanda ya hau karagar mulki a shekarar 1999, ya bayyana ƙarara cewa, sakamakon zai aika da saƙo ga ƙasashen yammacin duniya cewa, shugabanninsu sai sun yi la’akari da Rasha mai ƙarfin hali, ko a cikin yaƙi ko a cikin zaman lafiya, na shekaru da yawa masu zuwa.
Sakamakon zaɓen dai na nufin Putin mai shekaru 71 a duniya na shirin shiga wani sabon wa’adin shekaru 6 wanda zai sa ya wuce Josef Stalin wajen zama Shugaban Ƙasar Rasha mafi daɗewa a kan karagar mulki a cikin fiye da shekaru 200 idan ya kammala.
Putin ya lashe kashi 87.8 na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda shi ne sakamako mafi girma da aka taɓa samu a tarihin Rasha bayan Tarayyar Soviet, a cewar wata Gidauniyar Jin Ra’ayin Jama’a (FOM). Cibiyar Binciken Ra’ayin Jama’a ta Rasha (VCIOM) ta sanya Putin a kan kashi 87. Sakamako na farko a hukumance ya nuna sahihin zaɓe ne. Amurka da Jamus da Birtaniya da sauran ƙasashe sun ce zaɓen ba shi da ‘yanci ko adalci saboda ɗaure ‘yan adawar siyasa da kuma yin katsalandan.
Ɗan takarar Kwaminisanci, Nikolai Kharitonov, ya zo na biyu da ƙasa da kashi 4, sabon shiga Vladislav Davankov na uku, da Leonid Slutsky ɗan kishin ƙasa na hudu, sakamakon wani ɓangare ya nuna.
Putin ya shaidawa magoya bayansa a jawabin nasara da ya yi a birnin Moscow cewa zai ba da fifiko wajen warware ayyukan da ya kira “aikin soji na musamman” na Rasha a Ukraine kuma zai ƙarfafa sojojin Rasha.
“Muna da ayyuka da yawa a gaba. Amma idan muka haɗa ƙarfi da ƙarfe – duk wanda ya so ya tsoratar da mu, ya danne mu – babu wanda ya taɓa yin nasara a tarihi, basu yi nasara ba a yanzu, kuma ba za su yi nasara ba a nan gaba,” inji Putin.
Magoya bayansa sun yi ta rera taken “Putin, Putin, Putin” a lokacin da ya fito a kan dandalin da “Rasha, Rasha, Rasha” bayan ya gabatar da jawabinsa na ƙarɓar ragamar mulki.