Back

Radda ya ƙaddamar da ayyukan titi na naira biliyan 6 a ƙauyukan Katsina

Gwamna Dikko Radda yayin da yake ƙaddamar da ayyukan titi a ƙauyukan Katsina

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ƙaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 28 wanda aka gina naira biliyan shida a ƙaramar hukumar Kafur.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Dakta Bala Salisu-Zango, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Njeriya, NAN, a Katsina a ranar Litinin cewa gwamnatin tsohon gwamna Aminu Masari ce ta bayar da kwangilar wannan aikin.

Ya ce an tsara aikin ne domin buɗe jihar, inganta harkokin sufuri, da sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka.

Salisu-Zango ya ce titin mai tsawon kilomita 23.2 ya taso ne daga garin Kafur – Gurai – Buguwa-Sabon – Layi-Siran-Kahara-Mahuta, yayin da titin Gurai zuwa Rugoji ya kai kimanin kilomita biyar.

Ya ce gwamnatin Radda ta biya, ta kammala kuma ta ƙaddamar da aikin a Kafur. Ya ƙara da cewa, “mulki wani tsari ne da ake ci gaba da yi.”

Gwamna Dikko Radda zai kammala dukkan ayyukan da gwamnatin da ta gabata ta bayar. Ya ƙuduri aniyar biyan duk wasu lamurra na kwangilolin da gwamnatin da ta shuɗe ta bayar.”

Ya ce gwamnatin Radda ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa na tituna, don haka zuba jarin da ake yi a fannin don ƙara haɓaka rayuwar al’ummar jihar ne.

Ya ƙara da cewa gwamnan ya yabawa kamfanin bisa aiki mai inganci, sannan ya buƙaci jama’a da su kare hanya da sauran kayayyakin da aka samar a yankunansu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?