Back

Rahoton Oronsaye: Gwamnatin Tarayya ta kawar da fargabar asarar ayyukan yi

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya kawar da fargabar asarar ayyukan yi, wajen aiwatar da rahoton Oronsaye, wanda ke neman a daidaita ma’aikatun gwamnati da masu zaman kan su.

Idris ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba a taron manema labarai na ministoci karo na huɗu.

“Manufar ita ce gwamnati na son rage kashe kudade da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyuka. Ba wai yana nufin gwamnati na shirin korar ma’aikata ko jefa mutane cikin manema aiki bane,” inji shi.

Idris ya ce aiwatar da rahoton wanda ya shafe kusan shekaru sha ɗaya ba a yi amfani dashi ba, wata alama ce ta ƙarara na jajircewar Shugaba Tinubu na yin tattali a kasafin kuɗi da gudanar da mulki ta hanyar yin nazari mai zurfi a kan kwamitocin gwamnati, da hukumomi, da ma’aikatun gwamnati.

Ya ce amincewa da aiwatar da rahoton na Orosanye, wanda ya biyo bayan nazari mai zurfi, shi ne don tabbatar da cewa ba a yi ƙasa a gwiwa ba wajen aiwatar da muhimman ayyuka da kuma magance buƙatun ‘yan ƙasa yadda ya kamata tare da sanya buƙatun ƙasa a gaba.

“Ta hanyar aiwatar da rahoton Oronsaye, Shugaba Tinubu yana da niyyar cimma babban farashin tanadi ta hanyar kawar da kwafin ayyuka, daidaita tsarin gudanarwa, da inganta rabon albarkatu. Wannan tsarin zai baiwa gwamnati damar gudanar da aiki yadda ya kamata tare da kiyaye inganci da isar da ayyuka ga al’ummar Najeriya,” inji shi.

Ministan, wanda ya ce ‘yan Najeriya sun fara ganin alfanun sauye-sauyen da shugaban ƙasa ke jagoranta a sassa daban-daban, ya jaddada cewa, rahotanni daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), na nuni da cewa Najeriya ta samu ƙaruwar ɗaukacin darajan kayayyaki da aka samar na ƙasa (GDP) da kashi uku da ɗigo arba’in da shida a rubu’i na huɗu na shekarar da ta gabata saɓanin kashi biyu da ɗigo hamsin da huɗu da aka yi rikodin a cikin rubu’i na uku na shekarar da ta gabata.

Ya ƙara da cewa, rahoton na NBS ya kuma nuna cewa shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje ya ƙaru zuwa kashi sittin da shida cikin ɗari a rubu’i na huɗu na shekarar da ta gabata, lamarin da ya mayar da koma baya da kashi talatin da shida a rubu’i na uku. An rage shigo da man fetur da kashi hamsin tun bayan janye tallafin man fetur, yayin da Kasuwar Musanyan Hannayen Jari ta Najeriya ta haye maki dubu ɗari – mafi girma da aka taɓa samu.

Ya ce nasarorin da ake samu a tattalin arziƙin ƙasar ba wai kawai wani sa’a ba ne, amma musamman saboda sauye-sauyen da shugaban ƙasa ya ɓullo da su ne, wanda ya sa masu saka hannun jari su amince da tattalin arziƙin Najeriya.

Ministan ya ce, shugaban ƙasar ya kuma bayar da umarnin tsara shirin rashin aikin yi na jama’a domin kula da marasa aikin yi da kuma samar da tsarin bayar da tallafi na amfanin jama’a don bunƙasa ƙarfin siyan ‘yan Najeriya, yayin da suke yin sauye-sauye idan aka yi la’akari da wahalar tattalin arziƙi na wucin gadi.

Ya ce bayan sake duba shirin zuba jarin jama’a na ƙasa, shugaban ƙasa ya amince da a dawo da biyan Naira dubu ashirin da biyar kai tsaye ga gidaje miliyan sha biyar.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?