Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya roƙi gwamnatin tarayya da ta sauya shawarar da ta ɗauka na haɗe Jami’ar Sojin Najeriya ta Biu da ke Jihar Borno da Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) da ke Kaduna, kamar yadda rahoton Oronsaye ya bayar da shawarar.
Rahoton, tare da wasu shawarwari, ya buƙaci haɗewar sabuwar jami’ar soji da NDA da ta shafe shekaru da dama a Kaduna.
Zulum ya shaida wa manema labarai a Maiduguri, a ranar Alhamis, ashirin da tara ga watan Fabrairu, cewa, “Dukkanmu muna sane da cewa aikin farko na Boko Haram shi ne daƙile ilimin boko,” in ji Zulum, yayin da yake lura da cewa, “Haɗe Jami’ar Soja a matsayin wani sashe a Jami’ar NDA, tamkar taimaka wa ‘yan tada ne don cimma manufofin su.”
Ya ce, “Ina so in yi kira ga Shugaba Tinubu da ya janye shawarar haɗe Jami’ar Soja ta Biu da Kwalejin Tsaro ta Najeriya.”
Zulum ya ƙara da cewa, “Jahar Borno ta fuskanci mummunan rikici tun shekaru sha biyar da suka gabata, sakamakon haka, yawancin yaranmu sun kasa samun ilimi,” yana mai rokon, “Don haka wannan jami’a na da matuƙar muhimmanci ga al’ummar jihar Borno da ɗaukacin Arewa maso Gabas”.
Gwamnan ya jaddada cewa, “Ina kira ga shugaban ƙasa da ya duba wannan batu domin jami’ar soji ta Biu ta kasance mai cin gashin kanta,” ya ci gaba da cewa, “Idan har hakan ba zai yiwu ba, muna son yin kira ga shugaban ƙasa da ya ƙyale Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta karɓe jami’ar don zama jami’a ta al’ada.”
Zulum ya yi kira, “Idan zai yiwu, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta bar ta ta yi aiki a matsayin Jami’ar Soja, la’akari da muhimmancin ilimi a wannan yanki na ƙasar.”
Ya ƙara da cewa, “Ga dukkan adalci ga Gwamnatin Tarayya, wannan shawarar ta aiwatar da rahoton Oronsaye ya dace, musamman a halin yanzu da gwamnati ke ƙoƙarin dawo da tattalin arziƙin ƙasar.”
Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Duk da haka, mu mutanen Borno da Arewa maso Gabas, muna kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba matakin haɗe Jami’ar Soja da NDA.”
Ya ce jihar Borno a halin yanzu tana buƙatar ilimi fiye da kowane lokaci kuma jami’ar soji na da matuƙar muhimmanci wajen cimma hakan.
Bayan shekaru goma sha biyu na samun rahoton Stephen Oronsaye, a ƙarshe gwamnatin tarayya ta amince da aiwatar da wasu shawarwarin da rahoton ya bayar a ranar litinin domin rage farashin gudanar da mulki.
Rahoton ya kuma ba da shawarar cewa Cibiyar Fasaha ta Sojojin Sama ta zama jami’a a Kwalejin Tsaro ta Najeriya.