Gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa a ranar 9 ga Maris, 2024. Ta ce “ba gaskiya bane”.
Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki hayar wani mai sasantawa mai zaman kansa domin sasanta sakin yaran da aka sace a unguwar Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar lafiya.
Sai dai Muhammad Lawal Shehu, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Kaduna, ya ce a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau: “Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta ɗauki wani mai sasantawa ba, kuma ba ma tunanin yin hakan.
“Ɗaukar mai sasantawa mai zaman kansa ya wanzu ne kawai a cikin tunanin wakilin jaridar Punch. Gwamnatin jihar Kaduna na da kyakkyawar tsari kan rashin sasantawa da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
“Muna kira ga ’yan jarida da su yi taka-tsan-tsan kan yadda suke rubutawa da kuma yaɗa labaransu kan harkokin tsaro domin kada su kawo cikas ga ƙoƙarin da hukumomin gwamnati da na tsaro ke yi na ƙasƙantar da masu aikata laifuka da ke yiwa al’ummarmu kawanya.
“Idan da jaridar Punch ta yi ƙoƙarin tuntuɓar gwamnatin jihar Kaduna, da sun samu gamsassun bayanai, ‘yan jaridu abokan aikinmu ne a kullum, kofofinmu a buɗe suke.”