Back

Ramadan: Dangote ya raba buhunan shinkafa miliyan 1 a faɗin ƙasar, yana ciyar da mutane 10,000 a Kano

Alhaji Aliko Dangote

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya ƙaddamar da shirin rabon abinci kyauta, inda ake ciyar da musulmi kusan 10,000 a jihar Kano a cikin watan Ramadan.

Gidauniyar Dangote ce ke gudanar da shirin ciyar da abinci a jihar sa ta Kano, yayin da ake raba buhunan shinkafa miliyan 1 a faɗin ƙasar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar gidauniyar a Kano, Samira Sanusi, ta sanya wa hannu kuma ta miƙa wa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar Jigawa a ranar Litinin.

Ta ce, an kuma ƙara karimcin ne ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan 1, wanda kuɗinsu ya haura naira biliyan 13 a faɗin jihohi 36 na tarayya da Abuja domin rage yunwa a ƙasar.

Matakin, a cewarta, shine sauƙaƙa wa miliyoyin ‘yan Nijeriya wahala a cikin ƙalubalen tattalin arziƙi a ƙasar.

“Wannan baya ga rabon biredi 20,000 a kullum ga mazauna Kano da kuma 15,000 a kullum ga mazauna Legas, ciyarwar da aka fara kuma aka ci gaba da ita tun 2020 yayin ɓarkewar COVID 19.

“Abincin da ake dafawa na Ramadan kyauta ya haɗa da shinkafa jollof, farar shinkafa da stew, jollof spaghetti, doya, wake da kaza da naman sa, tare da kwalbar ruwa da lemo ga kowane mutum.

“Ana raba kayan abincin ne a masallatan Juma’a, tituna, gidajen yari, gidajen marayu, gidajen tsare, da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye,” inji Misis Sanusi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?