Back

Ramadan: Hisbah ta kama balagaggu 12 bisa ƙin yin azumi

Jami’an Hukumar Hisbah ta jihar Kano sun kama wasu balagaggu guda 12 da aka kama suna cin abinci da tsakar rana yayin da ake yin azumi.

Kamen ya biyo bayan wani samame da hukumar ta kai a wurare da dama da suka haɗa da kewayen Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad, Kofar Wambai, France road, Igbo road, Bata, Yankaba da kuma Kasuwar Mallam Kato.

Ana zargin mutanen da aka kama da ƙin azumi duk da sanarwar da gidajen rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai suka yi na ganin watan.

Sai dai waɗanda ake zargin sun ce suna cikin waɗanda ba za su yi azumi ba har sai sun ga wata da idanuwansu biyu kuma ba su da masaniyar sanarwar saboda ba su da rediyo ko wayar hannu.

Yayin da ɗayan ya amsa cewa ya ci rogo a cikin kasuwa, wani kuma ya ce ya samu ciwon gyanbon ciki, shi ya sa ya ci abinci.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Dakta Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce za a ci gaba da kai samamen a dukkan lungu da saƙo na jihar har sai kowa ya shiga azumin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?