
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya buƙaci malaman addini da su riƙa faɗawa masu mulki gaskiya ba tare da la’akari da alaƙarsu da shugabannin siyasa ba.
Gwamna Buni ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta yini ɗaya da manyan limamai da masu wa’azin addinin musulunci na ƙananan hukumomi 17 na jihar gabanin fara tafsirin Alkur’ani a watan Ramadan.
Gwamnan wanda mataimakinsa Idi Barde Gubana ya wakilta ya ce: ‘’Ya kamata ku yi mana wa’azi ku gaya mana gaskiya domin mu cika alƙawuran da muka ɗauka.
”Kada ku ji tsoron faɗin gaskiya. Ku ci gaba da tunatar da mu cewa dukanmu za mu mutu kuma mu bayyana a gaban Allah wata rana don yin lissafin aikinmu. Waɗannan za su canza tunaninmu daga dabi’un sata da rashin gudanar da mulki yadda ya dace.’’
A halin da ake ciki, Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya buƙaci malaman addinin Musulunci da su jagoranci mabiyansu wajen gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a jihar da ƙasa baki ɗaya.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kwamitin tafsirin watan Ramadan da Ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bidiah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta gudanar a Katsina a ranar Lahadi, gwamnan ya jaddada muhimmancin addu’o’i wajen magance matsalolin da yankin ke fuskanta a halin yanzu.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin Mai Taimaka Masa na Musamman kan Harkokin Addini (Izala), Malam Gambo Dan’Agaji, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa ayyukan addini saboda muhimmancin da suke da shi a harkokin addini da na duniya.
Shugaban taron, Alhaji Muhammad Usman Sarki, ya yi nuni da ƙalubale iri-iri da suka haɗa da rashin tsaro da wahalar tattalin arziƙi da jihar ke fuskanta, inda ya jaddada cewa addu’o’i na da matuƙar muhimmanci wajen rage raɗaɗin da jama’a ke ciki.