Back

Ramadan: Malamin addini ya ɗora wa shugabanni marasa tsoron Allah alhakin rashin tsaro da matsalar tattalin arziƙi

Shahararren malamin addinin Islama, Shaikh Dakta Kolawole Juma’a, ya ɗora alhakin matsalolin tsaro da tattalin arziƙi da Nijeriya ke fuskanta a kan waɗanda ya bayyana a matsayin shugabanni marasa tsoron Allah.

Malamin ya koka da cewa shugabannin siyasar ƙasar nan da alama ba sa tsoron Allah, mahaliccinsu, ko kuma ranar sakamako.

Shaikh Juma’a ya zanta da ‘yan jarida kai tsaye bayan laccar sa na Tafsirin Ramadan, wanda Gidauniyar Jin Daɗin Musulunci, reshen jihar Kwara ta shirya kuma wanda aka gudanar a Owoniboys da ke kan titin Ibrahim Taiwo, Ilorin.

Ya yi mamakin dalilin da ya sa duk da jami’an tsaro daban-daban a Nijeriya, har yanzu matsalar rashin tsaro ta ci gaba.

Ya gargaɗi masu kula da harkokin tsaro da tattalin arziƙin ƙasa da su guji fushin Allah da azabar ranar sakamako.

“Waɗanda suka yi imani da hisabin lahira ne kawai za su zage damtse wajen ci gaba da shugabanci na gari da adalci. Za su ji tsoron Allah a cikin ayyukansu da sauransu.

“Rashin imanin shugabannin siyasa na yanzu da lahira shi ne babban dalilin ayyukansu da yanke shawarar su.

“Rashin imani da ranar da za a yi musu hisabi ya sa su fifita buƙatunsu fiye da jin daɗin ƙasar.”

Ya buƙaci musulmi da su ci gaba da yi wa shugabanninsu da al’ummar ƙasar addu’a, tare da cewa Allah zai amsa addu’o’in ‘yan Nijeriya.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?