Back

Ramadan: Maryam Abacha ta buƙaci gwamnatoci da su bada tallafin abinci ga mabuƙata

Hajiya (Dakta) Maryam Abacha

Uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha, Hajiya (Dakta) Maryam Abacha, ta yi kira ga gwamnoni da sauran masu hannu da shuni a ƙasar nan da su saya kayan abinci domin tallafa wa mabuƙata, musamman a wannan mawuyacin lokaci yayin da watan Ramadan ke gabatowa.

Hajiya Maryam ta bayyana hakan ne ga manema labarai a Abuja a taron tunawa da ɗanta Abdullahi da ya cika shekara ɗaya da rasuwa.

Ta yi nuni da cewa a halin yanzu mutane da dama na cikin tsananin buƙatar taimako, ta kuma yi kira ga gwamnoni da su yi amfani da ƙarin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta bayar domin yi wa al’ummar mazaɓarsu hidima.

“Ina kira ga gwamnati da sauran jama’a da su taimaka wa mabuƙata. Jama’a da dama na fuskantar matsalar kuɗi, kuma duk da cewa ana samun abinci a kasuwa, amma ya kan yi tsadar da ba za su iya biya ba,” inji ta.

Ta kuma jaddada cewa, “Ina roƙon masu hannu da shuni da gwamnati da su ba da tallafi. Na fahimci cewa shugaban ƙasa ya ware maƙudan kuɗaɗe ga Gwamnoni, wanda abin a yaba ne.

“Yana da muhimmanci a yi amfani da waɗannan kuɗaɗen yadda ya kamata, musamman don siyan kayan abinci don rarrabawa ga mutane masu rauni a cikin al’umma.”

“Waɗanda suke da hali su ba da taimako. Wannan ƙa’ida tana cikin Musulunci da Kiristanci. Idan muka yi amfani da waɗannan koyarwar, kowa zai amfana.”

Daga ƙarshe ta yi addu’a ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba al’ummar Arewa da Najeriya da ma duniya baki ɗaya sauƙi da lafiya, tare da bayyana fatan ganin watan Ramadan cikin ƙoshin lafiya

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?