Back

Ramadan: Shugaban NAHCON ya buƙaci al’ummar Musulmi su riƙa tallafa wa juna ta hanyar kyautatawa da tausayi

Shugaban NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi

Shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su taimaki juna ta hanyar kyautatawa, tausayi da fahimtar juna.

A cikin saƙonsa na Ramadan mai taken “Rungumar Juriya da Imani a wannan Ramadan”, wanda ya sanya wa hannu, Arabi ya ce: “Yayin da watan Ramadan ke ƙaratowa, ni a madadin Shugabanni da Ma’aikatan Hukumar NAHCON, ina miƙa gaisuwa da barka da azumin Ramadan ga ‘yan uwa musulmin Nijeriya.

“A cikin wannan lokaci mai tsarki na tunani da sadaukarwa, mu, a Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), muna so mu jaddada muhimmancin juriya da imani wajen fuskantar ƙalubale.

“Ya tunatar da musulmi muminai umarnin Alkur’ani da ya umurce su da su jure jarabawa daban-daban.

Shugaban ya yi nuni da cewa “Ana iya samun ƙalubale ɗaya ko biyu a tsakanin al’umma, amma wani ɓangare na imanin musulmi shi ne sanin cewa hikimar Allah tana cikin kowane fanni na rayuwa, ciki har da lokacin yunwa da wahalhalu, tare da juriya da haƙuri, rabawa da tausayawa.

“Ya ƙara da cewa: “Wata ne da ake buƙatar a tsananta addu’o’i don neman taimakon Allah a kowane fanni na rayuwarmu.

“Yayin da muka fara wannan ibada, mu haɗa kai mu samu tsima daga imaninmu ga Allah, mu sami ƙarfin juriya a fuskantar jarabawa.

“Lokaci ne da za mu taru a matsayin al’umma, muna tallafa wa juna ta hanyar kyautatawa, tausayi da fahimta.

“Ramadan ya zama abin tunatarwa cewa sadaukarwar da muka yi na juriya na ƙarfafa alaƙa mai zurfi da Allah da kuma fahimtar haɗin kai.

“Muna ƙarfafa dukkan Musulmin Nijeriya da su rungumi Ramadan da zuciya ɗaya, tare da fahimtar cewa ƙalubale dama ce ta ci gaba da kuma ƙarfafa imani.

“Allah ya sa wannan wata ya zama tushen albarka, zaman lafiya, da kuma sabunta azama ga kowa da kowa.

“Ramadan Mubarak zuwa ga al’ummar Musulmin Nijeriya baki daya.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?