Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Zamfara ta yamma, Alhaji Abdulaziz Yari, ya ƙaddamar da rabon tirela 358 cike da kayan abinci, da ya bayar ga marasa galihu a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Magidanta 17,500 masu rauni ne za su ci gajiyar wannan karimcin a faɗin jihar.
Hatsin na ƙunshe a tireloli 358 na kayan abinci iri-iri da suka haɗa da shinkafa, gero, sukari da masara ga al’ummar jihar ba tare da la’akari da manufar siyasa ba.
Yari wanda ya yi magana ta bakin Shugaban Kwamitin Raba Kayan Ramadan na Yari, Sanata Tijjani Yahaya, a yayin taron da aka gudanar a garin Talata Mafara, hedikwatar ƙaramar hukumar Talata Mafara a ranar Litinin, ya bayyana cewa an yi hakan ne domin baiwa waɗanda suka ci gajiyar tallafin damar fara ibada cikin sauƙi.
“A ƙarƙashin wannan tsari, gidaje 17,500 a kowace ƙaramar hukuma 13 cikin 14 na jihar za su karɓi waɗannan kayayyakin yayin da ake shirin kaiwa gidaje 22,500 a ƙananan hukumomin Gusau,” inji shi.
Sanata Yari ya buƙaci masu arziƙi a tsakanin al’ummar Musulmi da su yi amfani da watan Ramadan wajen taimaka wa marasa galihu da ke yankunansu domin rage musu halin ƙunci.