Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya ƙaddamar da bayar da rancen naira miliyan 500 ga ma’aikatan gwamnati a bikin Ranar Mayu a Kaduna.
Gwamnan ya ce nan ba da daɗewa ba za a ƙaddamar da wasu shirye-shirye na ƙarfafa tattalin arziƙi ga ma’aikatan jihar.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa da ƙungiyoyin ƙwadagon cewa gwamnatin jihar ƙarkashin jagorancinsa za ta ci gaba da baiwa ma’aikata fifiko tare da samar musu da kayan aiki yadda ya kamata, inda ya bayyana cewa ƙwazon ma’aikata na da matuƙar muhimmanci wajen cimma burin gwamnatinsa na kawo sauyi a karkara.
Da yake magana a kan taken bikin ranar Mayu na bana, wanda shi ne ‘Mutane Farko’, Sani ya ce, ci gaba ya shafi jama’a ne, kamar yadda kuma mulki ya shafi jama’a.
“Mun ƙulla dabarun haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙwadago domin ciyar da buƙatun ma’aikata da inganta rayuwar talakawa da marasa galihu a Jihar Kaduna. Ƙungiyoyin Ƙwadagon sun shiga cikin dukkan kwamitocin mu kan rabon kayan abinci.”
“A cikin shirye-shiryen inganta tattalin arziƙinmu ga ma’aikatan Jihar Kaduna, mun fara aiwatar da shirin bayar da lamuni na naira miliyan 500. Nan ba da jimawa ba za a ƙaddamar da wasu tsare-tsare na ƙarfafa tattalin arziƙi ga ma’aikata a Jihar Kaduna. Muna jawo jari don samar da guraben ayyukan yi ga ’yan jihar mu. Muna horar da ma’aikata tare da sake horar da su don sanya su a wuri mai kyau don ba da gudummawa yadda ya kamata ga ci gaban tattalin arziƙin jiharmu mai daraja”.
Ya bayyana cewa gwamnoni a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya suna tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago a matakin tarayya da na jihohi, domin samar da ƙarin albashi mai inganci kuma mai karɓuwa ga ma’aikatan jihohi da ƙananan hukumomi.
Tun da farko, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya yabawa gwamnan bisa halartar bikin Ranar Mayu da kan sa, inda ya ce ƙungiyar ƙwadago ba ta shaida kasancewar gwamna a irin wannan taron ba tsawon shekaru tara.
A yayin da ya yaba wa gwamnan kan yadda ya ba da fifiko kan jin daɗin ma’aikata ta hanyar biyan albashi da alawus-alawus, da kuma shigar da ƙungiyoyin ƙwadago wajen yanke shawara a jihar, Shugaban NLC ya bayyana fatan ma’aikata za su samu kyakkyawan yanayin aiki a tsawon mulkinsa.
“Buƙatunmu su ne gwamnati ta ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa aƙalla naira 200,000, ta inganta tattalin arziƙi, ta magance ƙarin farashin man fetur da kuma ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan, a ƙarshe, batun rashin tsaro domin idan babu tsaro, ba za a samu ci gaba mai ma’ana ba,” inji shi.