Back

Ranar Rediyo ta Duniya: Gwamnatin Tarayyar ta yi alƙawarin tallafawa gidajen rediyon al’umma

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi alƙawarin faɗaɗa gidan rediyon al’umma a matsayin wani makami na ƙarfafa dimokuradiyyar ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata don tunawa da ranar rediyo ta duniya.

Ana bikin ranar rediyo ta duniya kowace shekara a kowace a ranar Sha uku ga watan biyu.

Taken bikin na bana mai suna, ‘Radio: Ƙarni na faɗakarwa, nishadantarwa da ilmantarwa,’ “yana nuna gagarumar nasarar da rediyo ya samu a matsayin hanyar sadarwa da bayanai sama da shekaru dari da suka shude, duk da zuwan kafafen sada zumunta,” a cewar Idris.

Ministan ya lura cewa rediyo yana taka muhimmiyar rawa wajen yin tasiri akan ra’ayin jama’a da kuma inganta haɗin kan al’adu a cikin al’ummar mu mabanbanta,” ya ƙara da cewa yana ba da “kafa ga mutane daga kowane usuli domin yin magana, a ba su wakilci, a saurare su, ba tare da la’akari da ƙabilar su, addinin su, ko alaƙar su ta siyasa ba.”

Idris ya bayyana cewa saboda yaɗa labaran da rediyon ke yi, “gwamnati ta ɓullo da sauye-sauyen da suka dace wajen kafa gidajen rediyon al’umma.”

Yayin da Najeriya ke da gidajen rediyon al’umma 89 masu lasisi, ministan ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a shirye take ta samar da yanayi mai kyau ga wasu gidajen rediyon su ɓullo, kuma a lokaci ɗaya, za a ƙarfafa waɗanda aka riga aka kafa.

Sanarwar ta ce, “A yau, na bi sahun masu sauraron rediyo na duniya don murnar ranar rediyo ta duniya ta 2024 kamar yadda ƙasashe mambobin UNESCO suka ayyana kuma suka runguma a matsayin Ranar ta Duniya.

Taken na 2024 shi ne ‘Radio: Ƙarni na Faɗakarwa, Nishaɗantarwa da Ilmantarwa.’ Wannan jigon ya nuna gagarumin nasarar da rediyo ta samu a matsayin hanyar sadarwa da bayanai sama da shekaru 100, duk da zuwan kafafen sada zumunta. Kuma ya nuna alƙawarin samar da kyakkyawar gaba ga rediyo a matsayin kafar da ya tsaya tsayin daka shekara da shekaru.”

Idris ya bayyana cewa rediyo ya kasance “mahimmin hanyar sadarwa a Najeriya tun 1933. Iyawar sa na musamman na isa ga jama’a da dama ya sa ya zama hanyan da ya fi dacewa don yaɗa tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati zuwa kowane mataki na al’umma, ciki har da matakin tushe.

“Rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen tasiri akan ra’ayin jama’a da kuma inganta haɗin kan al’adu a cikin al’ummarmu mabanbanta.

Yana ba da kafa ga mutane daga kowane asali don yin magana, a ba su wakilci, a saurare su, ba tare da la’akari da ƙabila, addini, ko siyasa ba. A cikin ‘yan kwanakin nan, rediyon ya zama wata hanya mai ƙima ta magance rikice-rikice da kuma tushen fata ga waɗanda ake zalunta.”

Ministan ya lura da cewa “gwamnati ta amince da bambance-bambancen al’ummar Najeriya kuma ta amince da ƙarfin rediyo wajen isar da mutane cikin harsunan su. Don tabbatar da gidan rediyon al’umma ya zama abin dogaro, inganci, kuma mai araha, gwamnati ta bullo da sauye-sauyen da suka dace wajen kafa gidajen rediyon al’umma.

“A halin yanzu, tashoshi 89 ne kawai aka baiwa lasisin yaɗa labarai a Najeriya. Sai dai gwamnati na da niyyar sauya wannan yanayin ne ta hanyar samar da yanayi mai kyau domin wasu gidajen rediyon su ɓullo da kuma don waɗanda ake dasu su ƙarfafa ƙarfinsu don su bunƙasa.”

Idris ya yi kira da a saka hannun jari a gidajen rediyon al’umma, inda ya ƙara da cewa “ba shakka irin wannan jarin zai ƙarfafa dimokuradiyya, da inganta haɗin kan al’umma, da samar wa waɗanda ke zaune a yankunan karkara damar samun sahihin bayanai, daidai da Ajandar Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.”

Idris ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya “za ta haɗa kai da UNESCO don gudanar da waɗannan sauye-sauye da kuma bunƙasa ƙarfin da ake buƙata a fannin don ƙarfafa ikon rediyo na yaɗa sahihan bayanai masu inganci ga jama’a.

“Yayin da Najeriya ke murna da sauran ƙasashen duniya, ina kira ga ɗaukacin gidajen rediyo, na gargajiya ko na kan yanar gizo, da su gudanar da ayyukansu ta hanyar bin ƙa’idojin yaɗa labarai.

“Dole ne a tabbatar da ayyukan edita, irin su tantance gaskiya, haƙiƙanci, da daidaito, kafin a fitar da labarai. Dole ne mu tabbatar da gaskiya da amana da ke tattare da rediyo, wanda mafi yawan ‘yan Najeriya ke darajawa sosai.”

“A ƙarshe, ina taya masu sauraron rediyo murna kuma ina roƙon su da su yi amfani da rediyo don koyo, girma, da kuma sawa a ji muryoyinsu. Ina taya UNESCO murna don tunatar da mu amfanin da rediyo ke ƙara mana a rayuwa. Barka da ranar Rediyo ta Duniya!,” in ji Ministan.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?