Back

Rashin shugabanci shine babban matsalar Nijeriya, inji El-Rufai

El-Rufa’i

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce rashin shugabanci shine babbar matsalar Nijeriya.

El-Rufai ya bayyana haka ne a jawabinsa a taron ƙarawa juna sani na Manyan Jami’an Gwamnatin Jihar Borno.

An gudanar da shirin mai taken: “Haɓaka Ƙwarewar Jami’an Gwamnati wajen aiwatar da manufofi da sarrafa albarkatun ɗan adam”, a Maiduguri, babban birnin jihar a ranar Litinin.

Mallam Nasiru El-Rufai, wanda shine jagoran masu gabatar da jawabai a taron ya ce ya ziyarci Jihar Kaduna sau biyar ne kawai tun bayan da ya tafi kusan shekara ɗaya da ta wuce saboda baya son sukar shugabanni na da ko na yanzu.

“Abin da ba mu da shi shi ne shugabanci nagari, manyan abubuwan da ke tattare da ingantaccen shugabanci.

“Ya kamata shugaban ya samu mutanen kirki su yi aikin. Allah ne kaɗai zai iya yin komai da kanshi, komai iyawarka a matsayin shugaba, ba za ka iya yin tasiri kamar mutanen da ke kusa da kai ba.”

“Muna iya ganin cewa a Nijeriya, matsalarmu ɗaya ce kawai a Nijeriya, ba abinci ba, ba yunwa ba, ba farashin canji ba, ba cire tallafin man fetur ba amma rashin shugabanci ne,” inji shi.

El-Rufai ya ce ya ji daɗin abubuwan da ya gani a Maiduguri da wasu sassan Borno, inda ya ce wuraren sun samu sauƙi duk da rikicin Boko Haram da aka kwashe shekaru goma ana yi.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?