Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayar da shawarar a sake duba dokar makamai a Najeriya, a matsayin hanyar tinkarar matsalar tsaro da ta addabi kasar.
Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels cikin wani shiri “Sunday Politics,” ya ce kimanin bindigogi miliyan dari biyu ne ke yawo a cikin kasar Najeriya.
A cewar gwamnan, yawaitar bindigogi a Najeriya ne ya haddasa tabarbarewar tsaro da ke ci gaba da jefa al’ummar kasar a halin yanzu.
Gwamnan wanda tsohon dan majalisar dattawa ne ya bayyana cewa, a lokacin da yake majalisar, ya yi yunkurin gyara dokar ta bindigogi “saboda ta tsufa. Lokaci na karshe da aka yi wa dokar ta’addanci kwaskwarima a Najeriya ya wuce shekaru talatin da suka gabata”.
Gwamna Sani ya ce dokar bindigogi ta Najeriya bata dace da mafi kyawun tsarin irin dokokin na duniya ba.
A cewar shi, Najeriya ita ce kasa daya tilo “da za a iya kama ka da makami ba bisa ka’ida ba kuma a kai ka kotu sannan a iya sake ka bisa wasu tuhume-tuhume ba tare da an daure ka ba. Za ka iya biyan tarar kusan naira dubu hamsin a sake ka, ka koma gida.”
“Wannan ne ya sa na fara ba da muhimmanci wajen tsara dokar rike bindigogi a lokacin da cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Afirka, UNREC, ta gabatar da rahoto a lokacin da nake Majalisar Dattawa.”
“Rahoton na cewa kusan makamai miliyan dari biyu ne ke hannayen mutane ba bisa ka’ida sun kai a cikin ƙasa Najeriya, daga cikin adadin miliyan dari biyu da hamsin da ke yawo a yammacin Afirka,” in ji Sani.