Back

Rashin tsaro: Gwamna Radda yana neman tallafin Gwamnatin Tarayya

Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara tura jami’an tsaro zuwa jihar domin magance matsalar rashin tsaro.

An yi wannan kiran ne a lokacin da gwamnan ya ziyarci ƙauyen Wurma da ke ƙaramar hukumar Kurfi, kamar yadda wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Dakta Bala Salisu Zango ya fitar.

Kwamishinan ya ce Radda ya kasa haƙura da kukansa a lokacin da ya ziyarci ƙauyen domin jajanta wa mazauna ƙauyen kan harin da ‘yan bindiga suka kai kwanan nan wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu da dama.

“Gwamna Radda ya yi Allah-wadai da harin wanda ya bayyana a matsayin na dabbanci, inda ya ƙara da cewa abin takaici ne ganin yadda mutane suka bar ƙauyen sakamakon kashe-kashen rashin hankali da ‘yan bindiga suke yi.

“Gwamnan ya nanata ƙudurin gwamnatinsa na maido da zaman lafiya da tsaro a jihar, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta kashe kobo na ƙarshe a cikin baitul malin ta domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?