Back

Rashin Tsaro: Gwamnatin Kaduna za ta canza wa makarantu 359 wuri

Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana shirin mayar da makarantu 359 daga wuraren da ake fama da matsalar tsaro zuwa wasu al’ummomin jihar.

A ranar 7 ga watan Maris, ‘yan bindiga sun sace ɗalibai sama da 250 daga makarantar firamare ta LEA, Kuriga, inda aka sako 167 daga cikinsu makonni biyu bayan wani farmaki da sojoji suka kai musu.

Gwamnan, wanda Shugaban Ma’aikatansa, Sani Kila, ya wakilta, ya bayyana waɗannan matakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kuma taron horas da sabuwar Tawagar Kare Makarantu da aka kafa.

Wannan shiri, wanda wani ɓangare ne na shirin Gwamnatin Tarayya na Safe School Initiative, na da nufin inganta matakan tsaro don kare cibiyoyin ilimi, ɗalibai da malamai daga hare-haren da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ke shiryawa.

“Domin tabbatar da ilimi ga yaran da ke zaune a yankunan da ake fama da rikici da ‘yan ta’adda, gwamnati ta fara haɗe makarantu 359 da waɗanda ke a wurare masu tsaro,” inji Gwamna Sani.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?