Back

Rashin Tsaro: Hukumar sufuri ta Abuja, ta baiwa Nairaxi, Bolt Lasisi Domin Yin Ayyuka bisa yanar gizo

A wani mataki na magance matsalar rashin tsaro a babban birnin ƙasar tarayyar Abuja, Gwamnati, ta baiwa Nairaxi da Bolt lasisin gudanar da ayyukan tuƙi a yankin ƙarƙashin Tsarin ta na Kula da Sufurin Jama’a.

Yarjejeniyar ta bayyana Bolt da NAIRAXI a matsayin keɓaɓɓun masu gudanar da zirga-zirgar ababen hawa da aka ba su izini don samar da sufurin da ake buƙata da ayyukan sufuri ta hanyar amfani da manhajoji na waya a ”babban birnin.

Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar Sufuri ta FCTA ta wallafa ta hanyar Tsarin Kula Da Zirga-zirgar Jama’a a ƙarƙashin Hukumar Kula da Zirga-zirgar da Ababen Hawa (DRTS-FCT).

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ba da jimawa ba Hukumar za ta fara aiwatar da aikin tabbatar da doka a kan masu gudanar da aikin ba tare da bin ƙa’ida ba, ana sa ran wasu kuma za su fara ƙoƙarin samun lasisin su don gudun hana su aiki a babban birnin tarayya Abuja.

“Wannan yunƙuri na da nufin magance ƙalubalen rashin tsaro ta hanyar bibiyar bayanan da za a iya tabbatarwa da sauran fa’idodi masu mahimmanci a babban birnin ƙasar.

“Bayar da lasisin NAIRAXI da Bolt zai inganta tare da tsara yadda ake gudanar da zirga-zirgar ababen hawa ta yanar gizo tare da ɗaukaka mafi kyawun ayyukan sufurin a cikin Abuja.

“Hukumar FCTA za ta fara aiwatar da ayyukan tilastawa cikin gaggawa don murƙushe ma’aikatan da ba su da wannan lasisin a Abuja shirin Gudanar da Sufuri na Jama’a, an yi gargaɗin yiwuwar haramci ga ma’aikatan da basu da lasisin Gudanar da Sufurin Jama’a na FCTA.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?