Back

Rashin tsaro: Nijeriya abar kunya ce ga duniya, inji Janar T.Y Danjuma

T. Y. Ɗanjuma

Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Janar Theophilus Y. Danjuma, (rtd), ya ce matsalar tsaro da Nijeriya ke fuskanta ya sa ƙasar ta zama abar dariya da abar kunya ga duniya.

Janar Danjuma, yayin da yake jawabi a wajen Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Nwonyo na kowace shekara a ƙaramar hukumar Ibbi ta Jihar Taraba a ranar Juma’a, ya ba da shawarar cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa don magance matsalolin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.

“Dole ne hukumomin Nijeriya su ɗauki matakan gaggawa don dawo da martabar ƙasar ta hanyar magance matsalar tsaro da ke fuskantar al’ummar ƙasar,” inji shi.

Janar ɗin mai ritaya ya ci gaba da cewa babu wani mutum musamman ‘ɗan ƙasar waje da zai yarda ya zo ƙasar don saka hannun jari ko ziyartar wuraren yawon buɗe ido idan ba a tabbatar da tsaro ba.

“Babu wani mutum ko gungun mutane da za su so zuwa jiharmu ko ƙasarmu idan muka ci gaba da kashe kanmu da yanka kanmu,” inji shi.

Janar ɗin mai ritaya ya kuma koka da yadda ake fuskantar matsalar tsaro a faɗin Nijeriya, inda ya ƙara da cewa mummunan lamarin na buƙatar kulawar gwamnati cikin gaggawa.

Ya ce, “Wajibi ne masu riƙe da muƙamai su yi aiki tuƙuru domin samar da zaman lafiya a ƙasar ga dukkan ‘yan Nijeriya ciki har da ‘yan ƙasashen waje kafin mu samu ƙarin masu zuba jari a ƙasar.

“Idan muka ci gaba da sanya hanyoyinmu ba su da aminci ga jama’a su zagaya, ba za mu iya cimma burinmu na mai da Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Nwonyo ya zama bikin ƙasa da ƙasa ba.

“Abin takaici ne yadda Nijeriya ta zama abar dariya biyo bayan matsalar tsaro.

“Kamar yadda ƙasar ke a halin yanzu, mu abin kunya ne ga duk duniya don haka dole ne mu dawo da martabar mu kuma mu tsara gidanmu saboda a yanzu mun zama abin dariya ga duk duniya,” inji shi.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi aiki ba dare ba rana, domin samar da haɗin kai tsakanin jiharsa da Gwamnatin Jihar Taraba.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?