Bayan kashe mutane sama da 50 a wasu sababbin hare-hare da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai wasu al’ummomi a Jihar Binuwai da kuma matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan, shugabannin Majalisar Tarayya sun nemi ganawa da Shugaba Bola Tinubu cikin gaggawa.
A jiya Laraba ne Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin ganawa da Tinubu kan matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan, bayan sun yi muhawara kan sababbin kashe-kashe da aka yi a Jihar Binuwai.
An yi taron ne don samar da mafita mai ɗorewa ga kashe-kashen ta’addanci da ake yi a cikin ƙasar nan.
Har ila yau, majalisar ta buƙaci hafsoshi rundunonin tsaro da shugabannin sauran hukumomin tsaro da su gaggauta tura jami’an tsaro domin magance hare-haren da ‘yan ta’adda ke ci gaba da kaiwa a matsayin makiyaya a yankunan ƙananan hukumomin Kwande, Ukum, Logo da Katsina-Ala na Jihar Binuwai da nufin fatattakar su tare da dawo da zaman lafiya a cikin al’ummomin da abin ya shafa, da kuma saka hannun jari a fasahar sa ido da kayan aiki don ganowa da hana aukuwar hare-hare nan gaba.
Taron da ake shirin yi da shugaban ƙasar da kuma wasu ƙudirorin da ke zuwa bayan na farkon da majalisar ta yi, don ta sanar da shi rahotannin tarukan tsaro na majalisu na 8 da na 9 da kuma ƙudirorin da aka yi a baya-bayan nan tare da shugabannin tsaro.
Ƙudirorin sun biyo bayan wani ƙudiri ne da Sanata Emmanuel Udende (APC, Binuwai Arewa Maso Gabas) ya kawo a cikin al’amuran da ke da matuƙar muhimmanci ga jama’a bisa ga umarni na 41 da 51 na Majalisar Dattawa ta 2023 biyo bayan sababbin hare-haren da aka kai kan al’ummar Binuwai.
Da yake jagorantar muhawara kan ƙudirin, Sanata Udende ya koka da cewa aƙalla mutum 50 ne aka kashe a sababbin hare-hare a yankunan da lamarin ya shafa, inda ya ƙara da cewa a ranar Talata, 5 ga Maris waɗanda aka kai harin sun haɗa da Tyuluv, Borikyo, Kundav, Ugbaam, Uyam, Udedeku, Yaaiwa, Nyihemba, Tomatar, Menakwagh, Yiase da Agura, duk a Gundumar Sanata na Arewa Maso Gabas ta Binuwai.
Ya ci gaba da cewa, “Yanzu haka ‘yan ta’adda masu ɗauke da muggan makamai suna kai wa mazauna ƙauyukan da al’ummomin hari a kullum, kuma ana ci gaba da samun asarar rayuka yayin da suke shan wahala.
“Rahotanni sun ce ‘yan bindigar suna kashe mutanen ƙauyuka da dama, tare da ƙona gidaje kuma mazauna yankin da dama sun ɓata yayin da har yanzu ba a kama waɗanda suke aikata wannan aika-aika ba.
“Wannan mummunan yanayi ya jawo wa mata da yara da kuma tsofaffi wahala matuƙa, waɗanda ke tafiya mai nisa domin neman mafaka da kuma jiran matakin jami’an tsaro.”
Sanata Udende ya ƙara da cewa baya ga asarar rayuka da dukiyoyi, lamarin tuni ya yi illa ga tattalin arzikin al’umma da kuma haifar da ƙarancin amfanin gona, lamarin da ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da kuma hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan.
Ya yi mamakin cewa duk da koke-koke da jama’a da kuma ƙudirori da Majalisar Tarayya ta yi a baya dangane da ayyukan ta’addanci da waɗannan ‘yan ta’adda suke yi a matsayin makiyaya, da alama babu wani mataki na zahiri da gwamnati ta ɗauka na daƙilewa, ragewa ko kuma dakatar da ayyukan su gaba ɗaya.
Ɗan majalisar ya ci gaba da cewa, “Amfanin gwamnati shi ne tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma daidai da sashe na 14 (2)b na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara) kuma akwai buƙatar a ɗauki matakin gaggawa”.
A nasa gudunmawar, Sanata Osita Ngwu (PDP Enugu West) ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta nemi maslahar da ya kira ta siyasa ko al’ada domin magance matsalar tsaro kamar yadda Sanata Adamu Aliero (PDP Kebbi ta Tsakiya) ya nuna rashin jin daɗin sa da cewa duk da maƙudan kuɗaɗen da aka ware wa tsaro, da alama babu wani abu da za a iya nunawa game da shi, yana zargin rashin kulawar kwamitocin Majalisar Dattawa.
Ya bayyana takaicin cewa tuni ya gaji da zuwa domin nuna alhini kan asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba sakamakon hare-haren da masu aikata laifuffuka ke kaiwa.
Da yake magana a kan lamarin, Sanata Sadiq Umar (APC Kwara ta Arewa) ya ce shi ma ya gaji da zagayowar lamarin ba tare da samun mafita mai ma’ana ba kamar yadda kuma ya caccaki kwamitocin Majalisar Dattiwa da abin ya shafa.
Ya ce abin da Nijeriya ke buƙata shi ne a koma tushe, a ƙarfafa al’ummomin yankin da kuma aminta da su yadda ya kamata don magance matsalolin.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Lawan, wanda a halin yanzu yake riƙe da muƙamin Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, a tasa gudunmawar, ya shawarci shugabannin majalisar da su gana da Shugaba Tinubu, inda ya nuna cewa a ko da yaushe ana ba jami’an tsaro maƙudan kuɗaɗe a kasafin kuɗin ƙasar domin su tabbatar da tsaro.
Majalisar Dattawan, a wasu ƙudirori, ta yi kira da a sake nazarin tsarin tsaro a yankunan da abin ya shafa domin daƙile ci gaban hare-haren.
Ta kuma buƙaci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta gaggauta haɗa kayan agaji ga mutanen da waɗannan hare-hare suka raba da gidajen su a ƙananan hukumomin Kwande, Ukum, Logo da Katsina-Ala na Jihar Binuwai.