A ranar Asabar ne Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya ƙaryata iƙirarin da Gwamnatin Jihar Kano ta yi na cewa ya taimakawa tsohon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero, ya dawo jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya zargi Ribadu da taimakawa wajen dawo da tsohon Sarkin jihar ranar Asabar.
Gwarzo, a wata ‘yar gajeriyar hira ta faifan bidiyo a fadar sarkin da ke Gidan Rumfa, ya yi iƙirarin cewa Ribadu ya shirya jiragen sama guda biyu domin jigilar sarkin da aka sauke zuwa jihar.
Sai dai a wani martani da ya mayar a Abuja, kakakin ofishin NSA, Malam Zakari Mijinyawa, ya musanta zargin, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙarya, yana mai cewa ba gaskiya ba ne.
Mijinyawa ya dage cewa Mallam Ribadu bai bada jirgin da ya mayar da sarkin Kano ba.
Ya kuma buƙaci ‘yan siyasa da su riƙa lura da maganganunsu, domin suna iya kawo cikas ga ƙoƙarin hukumomin tsaro na wanzar da zaman lafiya a jihar.
A cewarsa, “Na karanta maganganun da ake yi a shafukan sada zumunta, ba gaskiya ba ne. Hukumar ta NSA ba ta yi safarar kowa a jirgin sama zuwa Kano ba.
“Ya kamata ‘yan siyasa su daina sanar da jama’a labaran ƙarya yayin da jami’an tsaro a jihar ke ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
Ku tuna cewa Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Lamido Sanusi, Sarkin Kano na 14 a ranar Juma’a, shekaru huɗu bayan da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta tsige shi.
Maido da Sarki Sanusi ya biyo bayan soke Dokar Majalisar Masarautu ta jihar 2019, wadda ta kafa masarautu biyar da sarakuna biyar masu daraja ta ɗaya.
Sai dai Babbar Kotun Tarayya ta hana gwamnatin jihar aiwatar da sabuwar dokar masarautar da ta mayar da Sanusi.