An shiga damuwa a yau Talata yayin da Sanatoci suka yi faman jiran Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya dawo da wutar lantarki jim kaɗan kafin a fara zaman majalisa.
Hakan ya jefa jan zauren majalisar cikin duhu yayin da ‘yan majalisar ke jiran a maido da wutar lantarki.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya fara zaman majalisar bayan an dawo da wutar lantarki daga baya.
Akpabio ya nemi afuwa kan matsalar da aka samu a zauren majalisar, inda ya bayyana cewa kusan ofisoshi tara har yanzu suna da matsalar rashin wutar lantarki yayin da ake ci gaba da aikin gyara lamarin.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) a watan Fabrairu ya yi barazanar katse wutar lantarki a Ma’aikatu, Sassa da Hukumomi (MDAs) har 86 kan bashin naira biliyan 47.1 da yake bin su.
Wasu daga cikin MDAs sun haɗa da Ma’aikatar Kuɗi, Yaɗa Labarai, Kasafin Kuɗi, Ayyuka da Gidaje; Bariki, Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Fadar Shugaban Ƙasa, Gwamnan CBN, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS), Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN), da kuma ofisoshin jihohi da ke Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT).