Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana a shirye ta ke ta sako fursunoni sama da 200 da aka wanke daga zargin alaƙa da ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram.
Sojojin sun kama fursunonin da aka wanke ne a samame daban-daban a cikin zazzafar rikicin Boko Haram a wurare daban-daban.
An ruwaito cewa za a miƙa waɗanda ake tsare da su ga gwamnatin jihar Borno domin a mayar da su cikin al’umma yadda ya kamata.
Taron, a cewar rahoton zai gudana ne a Barikin Giwa da ke Maiduguri, babban birnin jihar a ranar Talata.
“Aƙalla mutane 200 ne waɗanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne da jami’an tsaro suka wanke daga aikata wani laifi, za a miƙa su ga gwamnatin jihar Borno domin gyarawa da kuma mayar da su cikin al’umma.
“An shirya bikin miƙawar a safiyar yau (Talata) da ƙarfe 10:00 na safe a Barikin Giwa,” inji rahoton.
Rahoton ya ƙara da cewa Kwamishiniyar Harkokin Mata ta jihar, Zuwaira Gambo, da takwaranta ta na Yaɗa Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Tar Umar, za su karɓi waɗanda aka wanke a madadin gwamnatin jihar.