Rundunar Sojojin Saman Nijeriya (NAF) ta ce tana kan shirye-shiryen bikin cika shekaru 60 da kafuwarta da kuma “yin hidima wajen kare martabar Nijeriya.”
Wata sanarwa da kakakin hukumar NAF, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa bikin mai taken, “Rundunar Sojin Saman Nijeriya a Shekaru 60: Amfani da Haɗin Gwuiwa a Ƙirƙire-ƙirƙiren Jiragen Sama don Tsaron Yanki,” an shirya shi ne da jerin abubuwan da za a fara daga 14 zuwa 25 ga Mayu 2024.
Ya ce babban abin da zai fi ɗaukar hankali a wajen bikin ya haɗa da taro da baje kolin ƙasa da ƙasa na kwanaki 2, wanda za a gudanar tare da Taron Ƙungiyar Sojojin Saman Afrika Karo na Uku, daga ranakun 23 zuwa 24 ga watan Mayun 2024 a Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce a yayin taron, ana sa ran Manyan Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama na wasu ƙasashe, da manyan masu faɗa a ji a fannin tsaro, sarrafa jiragen sama da na sararin samaniya, da sauran masu ruwa da tsaki za su halarci bikin, domin samar da tattaunawa da haɗin gwiwa wajen ciyar da harkokin sarrafa jiragen sama gaba a nahiyar.
“Bikin zagayowar shekarar zai ƙarke da Fareti da nunin jiragen sama da za a yi a Sansanin NAF a Kaduna, a ranar 25 ga Mayu, 2024.
Har ila yau, ƙarshen zai bayar da yabo na musamman ga jaruman NAF da suka mutu, da waɗanda suka tsira da ransu, da kuma sadaukarwar da rundunar take yi na yi wa ƙasa hidima.
“Bugu da ƙari ga manyan abubuwan da za a yi, ɗimbin abubuwa masu ban sha’awa suna jiran masu halarta, gami da gasa mai ban sha’awa na Bincike da Ci gaba, ba da tallafin kiwon lafiya, gasar wasanni masu ƙayatarwa, da faretin jiragen sama don karrama wasu manyan jami’an NAF da suka yi ritaya kwanan nan,” inji shi.
Ya ce a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da abubuwan da za su faru sun cika ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, tare da rage farashi, NAF tana haɗa gwiwa da abokan tarayya da masu ɗaukar nauyi, a cikin gida da waje.
“Tallafin waɗannan abokan hulɗa da masu ɗaukar nauyi, ba shakka, yana nuna haɗin gwiwa wajen girmama ayyukan NAF da kuma samar da kyakkyawar makoma ga masana’antun tsaro da sarrafa jiragen sama a Nijeriya, Afirka da ƙetare.
Gabkwet ya ƙara da cewa “Yayin da NAF ta fara gudanar da wannan gagarumin biki, ana gayyatar al’ummar ƙasa da sauran al’ummar duniya da su shiga bikin cika shekaru 60 na sadaukarwa, dagewa da jajircewa wajen yi wa al’ummar Nijeriya hidima.”