Back

Rundunar ‘Yan Sanda A Kano Ta Ja Damara Wajen Samar Da Tsaro Lokacin Zanga-Zanga A Yau Da Gobe

Rundunar ‘yan sandan  jihar Kano, ta sanya jami’anta cikin shirin ko ta kwana gabannin zanga-zangar da ‘yan kungiyar kwadagon jihar suka yi shirin yi a yau ranar ishirin da bakwai da gobe ishirin da takwas ga wannan watan na Fabrairu.

Kwamishinan ‘yan sandan Jahar Hussaini Gumel, ya shaida a wata hira ta wayar tarho cewa tuni aka dauki matakan tsaro na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan jihar.

Ya ce an tura dakarun domin amincewa da zanga-zangar lumana wadda ba ta sabawa wasu dokoki na kasa ba, saboda kuma wani muhimmin hakki ne na ‘’yan kasa.

Kwamishina Gumel ya bayyana cewa an ba da umarnin gudanar da ayyuka masu tsari ga dukkan jami’an tsaro da kwamandojin yanki, kwamandojin dabaru, da jami’an ‘yan sanda na sassan kananan hukumomi arba’in da hudu na jihar.

Ya ce rundunar ta na aiki ne tare da sauran hukumomin tsaro a jihar domin tabbatar da cewa masu son gudanar da zanga-zangar sun gudanar ba tare da matsala ba.

“Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su samar da tsaro a duk wuraren da ake sa rai da tashe-tashen hankula, da suka hada da ofisoshin jam’iyyun siyasa, bankuna, wuraren kasuwanci, wuraren shakatawa da na motoci kafin muzaharar, lokacin da kuma bayan zanga-zangar.

“Ina ba da tabbacin kashi dari bisa dari ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda da su gudanar da ayyukan su na yau da kullum ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji Kwamishinan.

Ya ce jami’an tsaron wadanda za su kasance dauke da makamai za su sa ido a duk wuraren da aka san ya kamata domin tabbatar da cewa sun sun yi aikin su na samar da tsaro na lafiya da Kare dukiyoyin Jama’a yayin zanga-zangar.

Gumel ya bayyana fatan shi cewa matakan tsaro da aka riga aka kafa za su inganta zaman lafiya a tsakanin mazauna yankin a lokacin, da kuma bayan zanga-zangar.

Ya ce rundunar ba za ta amince da duk wani nau’i na tashin hankali a lokacin zanga-zangar da kuma bayan zanga-zangar ba saboda jami’an sun jajirce domin tunkarar duk wata barazana ta tsaro a ciki da wajen birnin.

Muna kira ga masu son yin zanga-zangar da su yi ta cikin wayewa yayin da muka tura kwararrun ma’aikatan mu kuma za su sanya idanu sosai a Lokacin.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?