Back

Rundunar ‘yan sanda za ta cire haramcin lasisin baƙin gilashin mota

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta yi nazari tare da gabatar da cire haramci a kan baƙin gilashin mota amma da tsauraran matakai na hana yin amfani da shi ta hanyar da bata dace ba da tabbatar da bin ƙa’idojin da suka shafi bayarwa da kuma amfani da shi.

Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce rundunar za ta horar da ma’aikatan Fasahar Bayanai da Sadarwa (ICT) da jami’an tsaro a duk faɗin ƙasar don bin ƙa’ida.

Samarwar Mai Taken: “Tsaron Cikin Gida: ‘Yan Sanda Sun Yi Bitar Bayar da Lasisin Baƙin Gilashi; Horar da Masu Nazartar ICT, Jami’an Aiwatarwa A Duk Faɗin Ƙasar,” 

Adejobi ya ce lasisin baƙin gilashin da aka gabatar zai ƙunshi abubuwa na musamman waɗanda zasu inganta aiwatarwa da kuma tsaro.

Sanarwar a wani ɓangare na cewa: “A wani yunƙuri na inganta tsaron ƙasa da kuma daƙile ayyukan ta’addanci da ake yi ta hanyar yin amfani da baƙin gilashi ta hanyar da bai dace ba, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kammala nazarin bayar da lasisin baƙin gilashin, wanda aka haramta a baya a watan Yunin 2022.

“An fara haramcin ne saboda fargabar da ake ta yaɗawa dangane da rawar da baƙin gilashi ke takawa wajen taimakawa munanan laifuka kamar satar mutane, fashi da makami, safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, safarar mutane da dai sauransu.

“Tare da shirin cire haramcin, ana aiwatar da tsauraran matakai don hana amfani ta hanyar da bata dace ba da tabbatar da bin ƙa’idojin da suka shafi bayarwa da kuma amfani da lasisin baƙin gilashi.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, an shirya horas da masu nazari na ICT da jami’an tsaro a duk faɗin ƙasar nan a ranar ashirin da tara ga watan Fabrairun 2024, a matsayin share fage na sake buɗe bayar da lasisin baƙin gilashi.

Ta ci gaba da cewa, “horon zai baiwa masu nazari na ICT da Jami’an Aiwatarwa ƙwarewa da ilimin da suka dace don tsara yadda za a yi rajista, da jagorantar masu rajista kan yadda ake amfani da shafin yanar gizo a inda ake buƙata, da kula da ƙorafe-ƙorafen jama’a, da kuma tabbatar da bin ƙa’ida yadda ya kamata.

“Zai mayar da hankali ne kan tsaurin sabbin ƙa’idojin, tare da jaddada muhimmancin tabbatar da daidaito tsakanin tsaron jama’a da ‘yancin kai a yayin da ake kiyaye tsaron ƙasa.

“Lasisin baƙin gilashi da aka gabatar zai ƙunshi abubuwa na musamman waɗanda zasu inganta aiwatarwa da kuma tsaro. Waɗannan sun haɗa da lambar QR da ke haɗe da babban na’urar kundun bayanai don tantancewa nan take, lambobi na musamman waɗanda ke da alaƙa da abin hawa da bayanan mai shi, don tabbatar da gaskiya da amana, da dai sauran matakan makamantan wannan.

“Yana da muhimmanci a nuna cewa ƙa’idojin bayar da lasisin baƙin gilashi da kuma amfani da baƙin gilashin za su bi tanade-tanaden ABABEN HAWA (HARAMCIN BAƘIN GILASHI) na DOKAR 1991 da sauran dokokin da suka dace. Wannan hanyar ta jaddada yunƙurin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi na ba da fifiko ga tsaron jama’a yayin da take kiyaye haƙƙin jama’a da tsaron ƙasa.

“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta jajirce wajen samar da bayanai ga jama’a game da aiwatar da tsarin da aka yi bita na ba da lasisin baƙin gilashi, da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a ƙoƙarinta na tabbatar da tsaron cikin gida.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?