Back

Rundunar ‘yan sandan Nasarawa ta umurci ‘yan banga da su miƙa makamansu

Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta umurci dukkanin ‘yan banga da ke jihar da su miƙa makamansu da kakinsu su ga rundunar.

Umurnin ya biyo bayan matakin da Gwamnatin Jihar ta ɗauka na haramta duk wasu ƙungiyoyin ‘yan banga bayan wani taron gaggawa na tsaro da Gwamna Abdullahi Sule ya jagoranta.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Umaru Shehu Nadada, ya yi gargaɗin cewa ‘yan bangan da aka samu da makamai za su fuskanci hukuncin shari’a.

Ya ce, “Bayan Dokar Zartarwa Mai Lamba 1 ta shekarar 2024 da Gwamna Abdullahi Sule ya sanya wa hannu, wadda ta haramta duk wani gungun ‘yan banga da ke jihar, na kira taro da jami’an gudanarwa na domin roƙon waɗannan ƙungiyoyin da su gaggauta miƙa makamansu da kakinsu ga rundunar ‘yan sandan jihar.

Rashin yin hakan zai sa a kama su nan take kuma a gurfanar da su a gaban kuliya.

“Mun ƙuduri aniyar aiwatar da wannan haramcin kuma mun umurci dukkan kwamandojin yankin da su tabbatar da bin dokar cikin wa’adin makonni biyu da gwamnatin jihar ta bayar.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?