Back

Sakataren wajen Amurka, ya fara ziyarar Gabas ta Tsakiya don neman sulhu tsakanin Isra’ila da Hamas

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya isa ƙasar Saudiyya ranar litinin domin ziyarar rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya, da fatan ganin an cimma wata sabuwar yarjejeniya a yakin Ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da Hamas, ganin cewa Gaza har yanzu ba ta daina faɗan ba.

A ziyarar sa ta biyar zuwa yankin tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar bara, Blinken ya sauka a Riyadh daga baya Kuma ana sa ran zai ziyarci Isra’ila, Masar da Qatar.

Gabannin tafiyar sa, ya jaddada buƙatar “gaggauta magance buƙatun jin ƙai a Gaza”, bayan ƙungiyoyin agaji sun sha yin kakkausar murya kan mummunan tasirin da yaƙin ya yi na kusan watanni huɗu a yankin da  kewaye a wancan lokacin.

“Ba za a iya misalta lamarin ba,” in ji Said Hamouda, wani Bafalasɗine wanda ya tsere daga gidansa a zirin Gaza zuwa kudancin birnin Rafah da ke kan iyaka da Masar.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi wa yaƙin laƙabi da “halin yanke kauna”, yanzu Rafah ta karɓi baƙuncin fiye da rabin al’ummar Gaza, waɗanda suka rasa matsugunan su saboda harin da Isra’ila ta kai.

A ƙarshen mako, Isra’ila ta ƙara matsawa kudu zuwa birnin kan iyaka mai cike da cunkoson jama’a, tana mai gargaɗin cewa dakarunta na ƙasa za su iya tunkarar Rafah a matsayin wani ɓangare na yaƙin kawar da sojin Hamas.

Majiyoyi sun shaidawa Kamfanin Dilancin Labaren AFP cewa suna iya jin ƙarar harbe-harbe a yankunan gabashin Rafah da Khan Yunis, inda Isra’ila ta yi imanin cewa wasu manyan jami’an Hamas na ɓoye.

Ofishin yaɗa labaran gwamnatin Hamas ya ce an ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a tsakiyar ƙasar Isra’ila da kuma kudancin gabar tekun, ciki har da kusa da asibitoci.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?