Back

Sama da ‘yan Nijeriya miliyan 6 ne rashin tsaro da bala’i ya raba da muhallansu, inji Gwamnatin Tarayya

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa (NCFRMI) ta bayyana cewa sama da ‘yan Nijeriya miliyan 6 ne suka rasa matsugunansu sakamakon rashin tsaro da bala’o’i.

Kwamishinan Tarayya na NCFRMI, Alhaji Tijjani Aliyu ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai wa Gwamna Dikko Radda a jihar Katsina ranar Juma’a.

A cewarsa, ya zuwa shekarar 2022, hukumar tana da mutane kusan miliyan 3 da suka rasa matsugunansu, “amma tare da ambaliya da sauran bala’o’i, yanzu muna da ƙarin kashi 100 na irin waɗannan mutanen da suka rasa matsugunnansu.

Ya yi bayanin cewa: “A yau, a bisa hukuma zan iya cewa muna da ‘yan Nijeriya sama da miliyan 6 da suka yi gudun hijira daga gidajensu.

“Me za mu yi idan dukansu ba za su iya komawa ba, ta yaya za mu kula dasu? Shin gwamnati za ta iya ci gaba da ciyar da su, tana ba su taimako?

“Ba zai yiwu ba, dole ne mu nemo hanyar da za mu koya wa waɗannan mutane sana’o’i, mu ba su ƙwarewa, ta yadda a ƙarshe zasu iya kula da kansu,” inji shi.

Aliyu ya bayyana aniyar hukumar na gina manyan cibiyoyi guda uku na koyar da sana’o’i a yankin Arewa maso Gabas, daga kasafin kuɗin shekarar 2024/2025.

Ya ce manufar ziyarar ita ce raba kayan abinci ga mutane kusan 700 da suka rasa matsugunansu a jihar.

“Kafin yau, hukumar ta yi ƙoƙarin ganin ba a bar waɗannan mutane a wulaƙance ba. ‘Ya’yansu sun samu kuɗin karatu a wurinmu.

“Kimanin 120 daga cikinsu an horar da su, sannan kuma kusan 70 daga cikin iyayensu mata an ba su wasu ƙananan jari don fara inganta rayuwarsu,” inji shi.

Aliyu ya ce baya ga haka, hukumar ta gano matsalar ruwa a sansanin ‘yan gudun hijira amma nan take ta shiga tsakani ta hanyar samar da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana.

“Mun kuma gina wuraren zama a sansanin ‘yan gudun hijira, ga waɗanda ba za su so komawa gidajen kakanninsu ba, kuma Katsina na ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana,” inji shi.

Shugaban NCFRMI ya ce hukumar ta kuma ƙudiri aniyar shigar da ‘yan gudun hijirar cikin tsarin inshorar lafiya domin kula da matsalolin kiwon lafiyar su.

Da yake mayar da martani, Gwamna Radda ya yaba wa matakin da hukumar ta ɗauka, inda ya bayyana ta a matsayin wani nauyi da ya rataya a wuyan gwamnatin jihar da na tarayya wajen tabbatar da walwala da jin daɗin ‘yan gudun hijirar.

Ya ce a baya-bayan nan jihar ta fuskanci ƙalubalen tsaro da dama musamman a ƙananan hukumomi takwas na jihar.

Gwamnan ya koka da cewa wuraren da lamarin ya fi shafa su ne kwandon abinci na jihar, inda ya ce galibin al’ummomin sun yi gudun hijira.

Radda ya nuna gamsuwa da yadda aka ƙaddamar da hukumar tsaro ta Katsina Security Watch Corps (SWC), lamarin tsaro ya inganta.

A yayin da yake roƙon ƙarin haɗin kai da jihohin da ke maƙwabtaka da shi, gwamnan ya bayyana fatansa cewa da ƙarin jami’an tsaro da gwamnatin tarayya ta yi a baya-bayan nan, ba za a bai wa masu aikata laifukan wurin numfashi ba.

Daga ƙarshe kwamishinan na tarayya ya jagoranci sauran jami’an ƙasar wajen ƙaddamar da rabon kayan abinci ga ‘yan gudun hijirar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?