Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa rashin biyan sama da Naira tiriliyan uku da take bin kamfanonin iskar gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ne ke haddasa ƙarancin wutar lantarki a ƙasar.
Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adebayo, ya ce gwamnati na bin kamfanonin iskar gas dala Miliyan Daya da dubu dari uku ($1.3) yayin da take bin kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) Naira biliyan daya da dubu dari uku (1.3).
Ministan ya bayyana cewa ƙarancin wutar lantarki a halin yanzu ya samo asali ne saboda kamfanonin iskar gas da suka nemi bashin da ake bin su kafin su samar da sabon haja ga GenCos.
Ya kuma ce gwamnati ta yi kasafin Naira biliyan ɗari huɗu ne kawai a shekarar 2024 don biyan tallafin wutar lantarki yayin da ake hasashen kuɗin ya kai Naira tiriliyan 2.9.
“Matsalar da muke fuskanta a yanzu shine matsalolin kuɗi da ke fitowa daga tsarin harajin da bai dace ba, rashin karɓar harajin da kuma rashin isassun kuɗaɗe na tallafin gwamnati wanda ke haifar da ɗimbin basussuka da ake bin kamfanonin rarrabawa, samarwa da na iskar gas.”
Wannan ya hana saka hannun jari da ake buƙata don ɗorewar samar da wuta, faɗaɗa adadin samarwa da inganta ababen more rayuwa. Hakan kuma ba wai kawai ya hana ba da lamuni ga fannin daga cibiyoyin hada-hadar kuɗi kasancewar ayyukan fannin babu riba ba, har ma ya sa ɓangaren ya zama mara ban sha’awa ga sabbin masu zuba jari.”
Ya ce don inganta fannin, gwamnati na buƙatar “biyan wasu basussukan da ke akwai ga kamfanonin samar da iskar gas da na wutar lantarki ta hanyar biyan wani ɓangare na kuɗaɗen da kuma hanyoyin biyan bashi masu garanti.
Naira tiriliyan 1.3 ne bashin da ake bin GenCos a halin yanzu yayin da Dala biliyan daya da Miliyan (1.3) shine tsohon bashin da ake bin kamfanonin wutar lantarkin. (GenCos.)”
Ya kuma ce babban matsalar da ke damun ɓangaren shi ne rashin bayyana ma’anar mu a kan wutar lantarki a matsayinmu na ƙasa baki ɗaya.
“Shin samfurin kasuwanci ne ko sabis na al’umma?
Wannan ya kai ga gurɓataccen tsarin haraji tare da rashin tallafin gwamnati wanda ya ƙarke da manyan basussuka waɗanda ke hana ci gaba da ɗorewar hanyar samarwa. A gaskiya muna buƙatar tattaunawa ta ƙasa kan wannan matsalar ta ƙarshe.”
Yayin da ya ke bayyana cewa gwamnati na duba batun sanya kuɗaɗe da kuma hanyoyin biyan bashi masu garanti don biyan basussukan, ya ce akwai buƙatar gwamnati ta duba yadda za ta samar da tallafin a fannin saboda ƙarancin kuɗi.
“Ba ina bayar da shawarar cire tallafin wutar lantarki ba ne, amma muna buƙatar mu duba yadda muke aiwatar da tallafin, abin da aka ware naira biliyan ɗari huɗu da hamsin ne amma muna yin hasashen naira tiriliyan biyu da Miliyan dari tara (N2.9) a matsayin tallafi. Har yanzu ba mu biya tallafin na Janairu ba. Na fahimci irin wahalhalun da ’yan Najeriya ke ciki don haka shugaban ƙasa ne ke da hurumin yanke hukunci kan yadda za a fito daga wannan.”