Sanatoci daga jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja ƙarƙashin Ƙungiyar Sanatocin Arewa, NSF, sun nesanta kansu daga kalaman Sanata Abdul Ningi kan kasafin kuɗin 2024.
A wata hira da Ningi ya yi a baya-bayan nan ya yi iƙirarin cewa Gwamnatin Tarayya na aiwatar da nau’i biyu na kasafin kuɗin 2024, iƙirarin da fadar Shugaban Ƙasa ta musanta ranar Lahadi.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, NSF ta bayyana cewa Ningi wanda shine Shugaban Ƙungiyar, ya bayyana ra’ayinsa ne kawai a iƙirarin da ya yi kan kasafin kuɗin 2024.
An yi nuni da cewa, ba a taɓa samun lokacin da suka gudanar da taro kuma suka umurci Sanata Ningi ya yi wa manema labarai jawabi a kan lamarin ba.
Sanarwar ta ce, “An gabatar da kasafin ne ga Majalisar Dattawa a yayin wani zaman haɗin gwiwa na majalisun biyu – Majalisar Dattawa da ta Wakilai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar 29 ga Nuwamba, 2023, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.
“Majalisun biyu na Majalisar Dattawa sun yi taka-tsan-tsan wajen gudanar da muhawara tare da zartar da shawarar Shugaban Ƙasa. Kuma Shugaban ya amince da shi, saboda ya gamsu da shi.
“A bayyane yake cewa Shugaban Ƙasa ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira Tiriliyan 27.5 ga Majalisar Dattawa ta Ƙasa kuma Majalisar ta zartar da kasafin kuɗi na Naira Tiriliyan 28.7 bisa la’akari da buƙatar yin ƙari ko ragi a cikin kuɗaɗen da aka ware na Ma’aikatu, Sassa, da Hukumomi, MDAs, daban-daban wanda yake daidai da ƙarfin ikon Majalisar Dattawa don aiwatar da muhimman ayyuka a sassa daban-daban.
“Saboda haka, maganar da Sanata Ningi ya yi cewa kasafin 2024 da Shugaban Ƙasa ya gabatar wa Majalisar Dattawa Naira tiriliyan 25 ne ba gaskiya bane, kuma bai kamata a ɗauki matakin a matsayin Ƙungiyar Sanatocin Arewa ba.
“A iyakar saninmu babu wani ƙarin kasafin kuɗi, duk abin da aka yi a kasafin kuɗin 2024. Maganar da Sanata Ningi ya yi na cewa an yi wasu abubuwa ra’ayin sa ne. Ba ra’ayin gaba ɗayanmu ba ne, Sanatocin Arewa.
“Saboda haka, mun raba kanmu daga matakin da ya ɗauka wanda ba shi da tushe balle makama.
“Mu Sanatocin Arewa muna goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma za mu ci gaba da ba shi goyon baya don samun nasarar magance matsalolin da ƙasarmu ke fuskanta.
Nijeriya, a wannan lokaci na musamman ba ta buƙatar ra’ayin ƙabilanci, sai dai haɗin kan kowa da kowa don kawo ci gaba a ƙasarmu Nijeriya.
“Za mu ci gaba da yin aiki tare da ’yan’uwanmu maza da mata daga kudancin ƙasar wajen ci gaban ƙasarmu don amfanin kowa da kowa.”