Back

Sanusi ya isa Gidan Gwamnatin Kano yayin da Fada ke jiran dawowar sa

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi, ya isa gidan gwamnatin Kano domin karɓar takardar naɗin shi tare da ci gaba da aiki a matsayin sarki ɗaya tilo a jihar.

An ruwaito cewa Sarkin ya isa Kano da yammacin ranar Alhamis kuma an shirya masa liyafar maraba da zuwa gida.

Ana sa ran zai kasance a ɗakin taro na Africa House da ke Gidan Gwamnatin Kano domin bikin naɗa shi da ƙarfe 10 na safe, inda zai wuce fadar Sarkin Nassarawa.

Daga nan ne Sarkin zai jagoranci sallar juma’a a Babban Masallacin Kano da ke fadar a ƙofar Kudu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?