Back

Sarkin gargajiya na Osun ya roƙi Tinubu kan buɗe iyaka da jamhuriyar Benin

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Oba Hameed Oyelude, Olowu na Kuta a ƙaramar hukumar Ayedire ta Osun, ya roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya sake buɗe iyakar ƙasar da jamhuriyar Benin.

Oba Oyelude, wanda ya yi wannan roƙo a wata tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Lahadi a fadarsa da ke Kuta, ya ce buɗe iyakar zai sauwaƙa wa ‘yan Nijeriya matsalolin tattalin arziƙi.

“A lokacin da aka rufe iyakar Jamhuriyar Benin, Gwamnatin Tarayya tana kare tattalin arziƙin ƙasar.

“Amma ina so in roƙi Shugaban Ƙasa ya duba yiwuwar sake buɗe iyakar don rage raɗaɗin ‘yan Nijeriya,” inji shi.

Oba Oyelude ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri da Shugaban Ƙasar, yana mai cewa yana nufin alheri ga ƙasar ta hanyar cire tallafin man fetur.

“Ribar cire tallafin man fetur na zuwa, amma mai yiwuwa ba nan take ba. Don haka ne ya kamata mu yi haƙuri da Shugaban Ƙasa.

“Bari mu baiwa wannan gwamnati lokaci. Ba shakka za mu isa wurin,” inji basaraken.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da kada ta ɗauki dukkan shawarwari da tsarin Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).

Oba Oyelude ya ce duk da cewa babu laifi wajen amfani da ra’ayoyi da tsarukan IMF a cikin gida, amma dole ne a yi hakan ta hanyar da za ta dace da ƙasar.

“Akwai koma bayan tattalin arziƙi kuma ƙalubale ne da muke fuskanta, amma na yi imanin za mu shawo kan lamarin a matsayin mu na ƙasa,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?