Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero, ya yi kira ga uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, da ta matsa wa mijin ta, Bola Tinubu, ya magance matsalolin gaggawa da ke addabar kasar nan kamar yunwa, da rashin tsaro.
Sarkin ya yi wannan rokon ne a lokacin da uwargidan Tinubu ta kai masa ziyara a Kano ranar Litinin
“Duk da cewa muna da hanyoyi da dama na isar da sako ga gwamnati kan bukatun mu amma hanyar ku, ta hanyoyin ku ita ce hanya mafi inganci da za ku iya bayyanawa shugaban kasa hakikanin abubuwan da ke faruwa a kasar,” haka sarkin, wanda ya yi magana ta bakin wani mai fassara, ya shaida wa uwargidan shugaban kasar.
Sarkin ya ce matsalar yunwa “ta zama mai firgitarwa kuma matsala ce mai bukatar a magance ta da gaggawa.”
Ya kuma bukaci uwargidan Tinubu da ta matsawa shugaban kasa don magance matsalar rashin tsaro.
“Batun rashin tsaro wata babbar matsala ce da muke fuskanta. Na san gwamnatin ku gada ta yi, amma ya kamata a dada tashi tsaye don a magance barazanar,” in ji Bayero.
Sarkin ya kuma bayyana damuwar sa kan shirin gwamnatin tarayya na mayar da ofisoshin hukumar kula da filayen jiragen sama na Najeriya da babban bankin Najeriya daga Abuja zuwa Legas.
Ya yi kira ga gwamnatin da ta fito ta yi bayyanin dalilan yin kaurar.
Sarkin ya kuma shawarci uwargidan shugaban kasan da ta ci gaba da shirin ta na “Renewed Hope Initiative.” wanda ke da nufin karfafawa ‘yan Najeriya marasa galihu gwiwa domin samun ci gaba.