
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Muhammad Sa’ad Abubakar 111, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da kada su rinƙa sukar shugabanninsu, a maimakon haka su yi musu addu’ar samun nasara wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Ya yi kiran ne a ranar Asabar a Lafiya domin tunawa da cika shekaru 5 da Sarkin Lafiya ya yi a kan karagar mulki a matsayin Sarkin Lafia na 17.
Ya bayyana cewa addu’a mai ɗorewa ce kawai za ta iya gyara al’amura a ƙasar nan, domin babu abin da shugabanni ke buƙata illa addu’a da nasiha mai kyau daga al’ummarsu domin samun nasara a aikin da ke gabansu.
“Ina roƙon dukkan ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a domin su yi aikin da aka ɗora musu da kyau,” inji shi.
Shima da yake magana, Shehun Borno, Abubakar Garbai El-Kanemi, ya bayar da shawarar a baiwa jami’an tsaro sahihan bayanai kan duk wani motsi da ake zargi.
Ya ce ƙasar na fuskantar ƙalubale da dama, kuma mafita ta dindindin ta waɗannan matsaloli guda biyu ne.
“Na farko dole ne mu yi addu’a ga Allah, na biyu dole ne mu samar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro,” inji shi.
El-Kanemi ya bayyana cewa bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro zai ba su damar gudanar da aikin da tsarin mulki ya ba su na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa yadda ya kamata.
“Sahihan bayanai za su taimaka sosai wajen taimakawa hukumomin tsaro wajen mayar da martani mai inganci ga barazanar rayuka da dukiyoyi,” inji shi.
A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya yabawa mai martaba Sarkin Lafia Sidi Bage Muhammad 1, na 17, bisa goyon bayan da ya bayar wajen ganin an samu nasarar dukkan shirye-shiryen gwamnati.
Ya ce babban nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati shi ne ta samar da ƙarin ci gaba, saboda haka, “Muna buƙatar addu’o’in ku domin mu samu nasara.
A martanin da ya mayar, Sarkin Lafiya ya yaba wa duk waɗanda suka zo daga nesa da na kusa don taya shi murna.