Ƙungiyar Kare Haƙƙokin Jama’a da Tattalin Arziƙi (SERAP) a ranar Lahadi ta ba Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani, da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wasu gwamnonin jihohi 35 wa’adin mako guda domin su ba da yarjejeniyar rance da kuma yadda aka kashe kuɗaɗen rancen da “jihohinsu da FCT suka karɓa.”
Hukumar ta kuma buƙaci “cikakkun bayanai da wuraren ayyukan da aka aiwatar da rancen,” wanda ya kai naira tiriliyan 5.9 da dala biliyan 4.6.
Ta ce buƙatar ta biyo bayan maganar da Gwamna Sani ya yi a ranar Asabar, inda ya koka da ɗimbin bashin da ya gada daga magabacinsa, Nasir El-Rufai.
Bashin, inji Sani, ya haɗa da jimillar dala miliyan 587, naira biliyan 85 da kuma bashin kwangila 115, kuma abin da ya rage a yanzu bai wadatar da biyan albashi ba.
Tare da bayyana hakan, SERAP ta nemi dukkan gwamnonin jihohi da kuma Ministan FCT da su ba da bayanan rancen su.
Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya bayyana haka a wata sanarwa a Abuja.
Ya buƙaci gwamnonin jihohi da Ministan Babban Birnin Tarayya su “wallafa kwafin” buƙatun su domin ‘yan Nijeriya su san yadda gwamnatocin jihohinsu ke kashe basussukan su, da kuma tabbatar da cewa “mutanen da ke da alhakin jama’a suna da alhakin yi wa jama’a bayanin yadda suke gudanar da ayyukansu na tafiyar da kuɗaɗen jama’a”.
Hukumar ta kuma yi kira ga gwamnonin jihohi da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya da su “gaggauta gayyato Hukumomin Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa na ICPC da EFCC da su binciki yadda aka kashe rancen gida da waje da jihohin ku da FCT suka karɓa.